Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Bukaci Iyaye Da Su Karfafa Karatun Alkur’ani Ga ‘Ya’yansu

Daga Shehu Yahaya

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da su runka sanya ‘ya’yan su a makarantu Islamiya domin rabauta da albarkar duniya da kuma lahira.

Sarkin ya bukaci hakan ne a wajan taron bude Karatun Musabakar karatun alkur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a makarantar koyar da harshan larabci ta S A S dake Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake bukatar al’umar jihar Kano da sauran Musulmi a ko ina suke a duniya su yawaita karatun Alkur’ani a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Mai Martaba Sarkin na kano ya kuma yi kira da mutane da su dukufa wajan yin addu’o’in samun zaman lafiya a lokutan zabe mai zuwa ayisu lafiya a gama lafiya tateda neman Allah ya zaba mana shugabanni nagari.

Ya kuma nuna damuwar sa a kan rashin shigar wasu Kananan Hukumomi cikin tsarin shirin Musabukar na bana.

Yace lallai wannan abune marar dadi, inda yayi fatan za’a bincika domin a fahimci dalilan da ya kawo hakan domin gyarawa a nan gaba.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamnatin jihar kano bisa daukar nauyin musabakar da take duk Shekara tareda bayar da dukkan gudumawar data kamata tun daga matakin kananan hukumomi zuwa ta duniya baki daya.

A nasa jawabi,shugaban hukumar Shirya musabakar al’qur’ani ta jihar Kano wanda shugaban kwamatin tsare tsaran musabukar Malam Abdurrahaman Tijjani ya wakilta ya ce, a bana kananan hukumomi hudu ne basu shiga cikin shirin musabakar ba da suka hadar da karamar hukumar Birni, Rogo Garin Malam da kiru da kuma Doguwa.

Leave a comment