Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci A Nijeriya yayi taronsa a Gombe da Bauchi

Wani Sashi na mahalarta taron

Daga Idris Umar,Zariya

Dandalin siyasa na harkar musulici a Najeriya karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ya gudanar da taruka na tsawon kwanaki 3 a cikin gida da na kaddamarwar.
(29 – 31 ga Oktoba, 2022).

Kungiyar ta kaddamar da daruruwan mambobinta wadanda za su dauki nauyin gudanar da ayyukan kungiyar a shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan.

An gudanar da tarukan ne a jihohin Gombe da Bauchi. Wakilai daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba na daga cikin wadanda suka samu jawabai masu zurfi a kan tsari da manufofi da ka’idojin da aka shimfida na dandalin. Wadanda suka halarci taron sun hada da Convener Sayyid Muhammad Ibrahim na kasa da kodineta kwamret Shuib Isa Ahmed da sauran masu ruwa da tsaki na dandalin.

Anyi taro lafiya antashi lafiya.

Leave a comment