Jarida Noblenews taba hisbah karamar hukumar Sabon Gari horo

Daga Idris Umar,Zariya

A ranar 21/11/2022.ne
(HISBAH) reshen Sabon Gari, COMMAND ta samu nasarar mammala taron bayar da horo akan harkar yanar gizo ta zamani wato (social media).

Babban bako wanda yabada shaidar kammala wannan horo(certificate) shine mataimakin kwamishinan yan sanda shiyyar Zaria, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa C.S.P Abdulraham Idris

Kwamandan Hisbah reshen karamar Hukumar ta Sabon Gari, Zaria Malam Abubakar Auwal yayi jinjina ga kamfanin Jaridar Noblenews bisa wannan horo da suka bayar kuma yayi Farin ciki tare da daukar alwashin za suyi amfani da dukkan dubarun da suka samu a lokacin bayar da horon yayin gudanar da aikin nasu a kowani lokaci.

Honorabul Aminu Yunusa na cikin manyan baki a gurin kammala wannan taro na yini guda.

Godiya ta musamman ga shugaban kamfanin Jaridar Noblenews U S Macika.

Rundunar Hisbah dai sashine dake taimako ta bangarori da dama musamman bangaren gyara tarbiyar al’umma a fadin karamar hukumar Sabon Gari da wasu jihohi a wannan kasa Nijeriya.

Tuni rundunar ta tabbatar da samun kulla zumunci da sauran takwarorin cibiyar tsaron dake fadin karamar hukumar ta Sabon Garin.

Bincike ya tabbatar da cewa jama’a na jin dadin aikinsu sosai bisa ga nuna adalci da sukeyi yayin gudanar da aikinsu.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment