Kano Da Jos Suna Da Tsohuwar Alaka Mai Karfi- Inji Sarkin Kano

Daga Shehu Yahaya

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL bayyana alakar zumunci dake tsakanin Masarautar Kano da Jos da cewa abune mai tsohon tarihi.

Mai Martaba Sarkin Kano ya bayyana hakan ne lokacin da yakai ziyara fadar Gbong Gwom Jos, Da Jacob Gyang Buba, CFR.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace garin na Jos tamkar gida ne bisa la’akari da dangantakar da magabata suka kulla, Inda ya tabbatar da cewa zai yadda cigaban wannan alaka ta zumunci tsakanin Kano da kuma Jos.

Yace ya zama waji su zama masu koyi da irin wannan kyakkyawan zumuncin da magabata suka kulla wajen girmamawa da mutanta juna, musamman da Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero yakeyi domin mutunta Masarautar da kuma al’umar garin na Jos.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Gbong Gwom Jos bisa yadda ya karbesu da karamci da mutuutawa, yace wannan abun a yaba ne kwarai da gaske.

Ya bukaci sauran Sarakunan Masarautar da su cigaba da bashi shawarwari masu kyau wadanda zasu kawo cigaban al’uma da Masarautar baki daya.

Sarkin na Kano yayi fatan wannan ziyara zata zama wata hanya ta Kara karfin dankon zumunci a tsakanin masarautun guda biyu da kuma al’umar jihar Kano da Filato.

Da yake Jawabi Gbong Gwom Jos, Da Jacob Gyang Buba, CFR ya godewa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa wannan ziyara da yakai masa fadarsa.

Gbong Gwon yace yace ba abun mamaki bane waannan ziyara Idan akayi laakari da irin dangantakar da take tsakanin magabatansu da kuma zumunci.

Ya bada tabbacin cewa zai cigaba da bayar da duk Wani hadin da goyon baya domin ganin cewa wannan dangantaka da take tsakanin masarautun biyu ta dore domin cigaban al’umar.

A Wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci taron bikin yaye Manyan Jami’an Gwamnati a cibiyar horar da Manyan Jami’an Gwamnati ta Kasa dake Kuru, a Jos dake jihar Filato.

Sa Hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano.
3/12/2022

Leave a comment