Da sauran mutanen zasu zama kamar irin almajiran Shiek Ibrahim El-Zakzaky a Nijeriya da munji dadi Inji —Rabaran Tijjani Cindo

Daga Idris Umar Zariya

A yau ne Almajiran Sheik Ibrahim El-Zakzaky na garin Samaru Zariya jihar Kaduna suka kai ziyarar muna da zagayowar haihuwar Annabi Isa(AS) a Cocin (CTBN) Church of the Brethren of Nigeria (Ekklesiyyar yan uwa) dake Samaru karamar hukumar Sabon Gari.

Farfesa Isa Hasan Mashalgaru ne ya jagoranci ziyaran.

A cikin jawabin Farfesan ya gayawa dubban mabiya addinin kiristancin cewa ziyarar tasu ta kunshi sada zumuncine zalla.

Kuma yace shugabansune Sheik Ibrahim El-Zakzaky ya koyar dasu hakan a shekaru masu yawa.

Ya kuma ja hankalin bangarorin biyu musulmi da kirista da kowa yaji tsoron Allah wajan gudanar da harkarsa don haka Allah ke so.
Farfesan ya karkare da Jan hankalin juna wanjan hadin kai a tsakanin juna yace a fadi tare a tashi tate a tsira tare ba tare da kyamar junaba kuma yayi farinciki da yadda cocin suka tarbesu hannu biyu biyu.

Shuganan Cocin Rabaran Tijjani John Cindo yayi wa almajiran na Sheik Ibrahim El-Zakzaky godiya tare da nuna jin dadinsa sosai harma ya kara da cewa da ace sauran mutane zasu zama kamar Almajiran El-Zakzaky da an sami zaman lafiya mai dorewa a kasa baki daya.

Shugana ya tabbatar wa Almajiran El-Zakzakyn cewa za suyi zumunci tare da ikon Allah.

Mawakan zumunta na cocin ne tare da Malam Dan Tinka Zariya ne suka gabatar da wake na tunawa da haihuwar Annabi Isa ( AS) anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment