Bazan mantaba da ABU Staff school ba —- Brigadier General Usman Lawal Abdullahi

.

Daga Idris Umar Zaria

Makarantar ABU Staff School Samaru Zariya sunyi taro tsoffin dalubai(ABUSSA 2022)

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halacci taron.

Taron an gudanar dashi ne a bubban dakin taro na jami’ar Ahmadu Bello dake Harabar makarantar wato ( Assembly Hall)

Farfesa Hahaya Kajuru shine shugaban taron.

An sami nasarar zuwan tsofin daliban duk da matsalar tsaro da ake fuskantar a fadin kasa baki daya.

An gabatar da mukaloli daban daban masu jawo hankali ga taimakon mafarin rayuwa da kawowa ita makaratar dauki tare nuni ga muhimmancin zumunci da taimakon juna ga dalubai.

Dakta Abullahi ya gabatar da mukala mai jawo hankalin akan muhimmacin koyan kananan sana’ar hannu mai makon dogaro da aikin gwamnati.

Shima Brigadier General Usman yana daya daga cikin mayan baki kuma tsohon dalibi a makarantar.

Birgedier General a jawabinsa ya nuna jin dadinsa sosai ya kumace bazai taba matawa da ABU Staff School ba domin itace ta zama foundation na samun duk wata nasara a rayuwarasa

kuma yace zai zanta da shugabanin makarantar na yanzu don ganin ya bayar da gudummawarsa kuma yayi kira ga sauran takwatorinsa na sauran bagarori da suzo su hada kai don kawo ci gaban makarantar

.

Brigadie General Usman yayi godiya ga dukkan tsofin malaman da daliban da ya hadu dasu a wannan taro.

Shima tsahon ministan aikin gona Farfesa Sheik Abdallah Dangi shima kira yayi ga daukacin tsoffin dalubai da karsu kuskura su manta da masomar rayuwa.

Kuma ya karkare da kiraga ga dukkan dalubai da su kara kwazo a dukkan inda suke.

Wakilin mai martaba Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli wanda hakimin Birni da kewaye ya wakiltar Barista Sambo Shehu Idris shima ya nuna jin dadinsa ne sosai da ganin wannan taro kuma yayi fatan alheri ga hukumar makarantar da tsofin daluban.

Ayi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment