MAI MARTABA SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO: Baƙon Shehu Maghili

Daga: Magaji Galadima

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar.

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har yazo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare masu muhimmanci a fadar Kano, kana kuma yayi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano dama nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes. A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Muma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sunyi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto dashi.

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hanasu shiga don a kyale Sarki ya huta.
A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida, ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya addu’oi na musamman.
A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022

Leave a comment