UBA SANI WIN PROJECT ta bayar da tallafin magani a Zariya

Daga Fatima Salis,Zariya

UBA SANI WIN PROJECT da UBA SANI ACTUALIZATION PROJECT sun gabatar da bayar da tallafin bayar da magani a garin Dogarawa dake a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Wakilinmu ya halacci taron.

Taron an gudanar dashine a makarantar Junior Secondary dake anguwar Dogarawa inda dubban mutane suka sami halanta.

Comrd Muktar Zubair shine Converner na wannan tafiyar ta UBA SANI WIN PROJECT.

Yayin yake kaddanar da bayar da magani ga al’umar Dogarawa ya baiyana cewa suna bayar da tallafinne don taimakon jama’a kamar yadda suka saba yi a lokutan baya karkashin tafiyar Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023 in Allah ya kaimu.

Comrd Muktar ya sha alwashin ci gaba da irin wannan hidima ga jama’a zarar anba mai gidansu goyon baya a zabe mai zuwa da ikon Allah.

Karshe yayi matukar farin ciki bisa yadda jama’a suka bashi goyan baya tare da amsa kiran da yayi masu.

Dakta Zaid Abubakar shine Grand Petron na wanan tafiya na (UBA SANI WIN PROJECT) shima ya sami zuwa wajan taron har ya sanyawa taron albarka tare da nuna goyon baya da fatan alher ga tafiyar.
Shima sarkin Dogarawa Alhaj Ahmed Usman ya sami zuwa wajan taron kuma yayiwa Comred Muktar Zubairu fatan alheri daya kawo wa jama’ar garin Dogarawa tallafin magani.

Wakilin mai martaba Sarkin Zazzau Ahmen Nuhu Bamalli Barista Ishak wakilin Yarbawan Zazzau shima godiya yayi da kira ga sauran masu hannu da shuni da suyi koyi da wannan abin alherin da UBA SANI WIN PROJECT ta kawoma jamar garin Dogarawa.

Dakta Tajuddin shi ne shugaban ayarin likitoci masu kula da harkar lafiya a tafiyar Dan takarar gwamnar jihar Kaduna shima ya gamsu da yadda UBA SANI WIN PROJECT suke gudanar da bayar da tallafin ga jama’a har yayi fatan Allah ya baiwa Dan takarar nasara.

Bincike ya tabbatar da cewa a kalla mutun 500 ne zasu amfana da tallafin maganin.

Haka zalika tallafin ya shafi gwaje-gwaje ne a bangarorin da dama tare da bayar da magani bayan tabbatar da irin lalurar dake damun wanda aka kwana.Malam Sani daga anguwar ta dorawa na daya daga cikin wanda aka gwana har aka bashi magani shima yayiwa Dan takarar fatan samun nasara.

An kaddamar cikin tsari da nasara.

Leave a comment