Sarkin Kano Aninu Ado Bayero Ya Bude Sabon Soron Ingila A Kano

Daga Shehu Yahaya

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya bude sabon ginin da aka sabunta wato Soron ingila, soron da ake Saukar manyan shuwagabanin duniya a duk lokutan da suka ziyarci Masarauta Kano.

Sarkin ya bude Soron Ingila ne bayan dawowarsa daga kasar ingila bisa ziyarar aiki da yaje kasar.

Soron ingila soro ne da Sarkin Kano Muhammmadu Abbas ya Gina shi a shekara ta 1903 bayan turawan mulkin malaka sun nada shi a matsayin Sarkin Kano.

Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya sake Gina soran a shekarar 1934 zuwa shekarar 1936 bayan dawowarsa daga kasar ta ingila, Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero lokacin da ya Zama Sarkin Kano ya mayar da soran ingila wajan Saukar manyan baki daga sassa daban daban na duniya a yayin da suka kawo ziyara Masarauta Kano.

Zamanin Sarkin Kano Murabus Muhammmadu Sanusi na 2 ya rushe soran ingila inda ya mayar da shi wajan hutawa.

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano na 15 a cikin jerin sarkunan fulani, inda ya sake Gina soran na ingila, yayin da ya gudanar da bikin bude shi a yau Litinin 23 ga watan Janairu shekara ta 2023 bayan dawowarsa daga wata ziyara a kasar Ingila.

Leave a comment