Mutane Sama Da Dubu 26 Suka sami tallafin magani daga honorabul Babawo a shiri na 7 yanzu ana cikin na 8

Daga Zahara Salis Zariya

Mai neman kujerar majalisar tarayya dake wakilatar karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna honorabul Garba Datti Babawo ya kaddamar da aikin bayar da tallafin magani kyauta tare da baiwa wasu asibitoci kayan aiki don karfafa kiwon lafiya a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari.

A lokacin da yake kaddamar da aikin bayar da tallafin maganin Dan majalisar ya tabbatar da cewa zuwa yanzu shirin bayar da tallafin ya yiwa masu lalurar ciwon kaba (Fibroids)kimamin mutum 1277 Operation kuma duk an sami nasara yin aikin.

Haka zalika Dan majalisar ya tabbatar da cewa shirin ya duba mutane masu fama da (melaria) da (Typhoid) da sauran ciwuwwuka fiye da mutum 25’259 a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari baki daya.

Kuma ya kara da cewa a wannan karon ya kawowa bubban asibitin Mejo Ibrahim Abdullahi memorial Hospital (LIMI HOSPITAL) kayan gudanar da aiki a cikin Asibitin na Naira miliyan 30 don amfanar mutanen karamar hukumar ta Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.

Karshe yayi fatan al’umar karamar hukumar zasu kara bashi goyon baya don karishe aikin da ya daukoyi a bangarori da dama a zabe mai tahowa

Daga cikin Mayan baki da suka rufawa taron kaddamar da bayar da tallafin maganin baya sun hada da honorabul Yusuf Shaka da honorabul Abubakar Albani da honorabul Nasiru Idi Kano da malamai da sarakuna da wakilan sashin lafiya na kananan hukumomi da yan takarkaru da sauran manya manyan yan jambiyar APC duk sun tofa albarkacin bakinsu da ya nuna goyan baya ga honorabul Garba Datti Babawo akan kokarin da yake yiwa al’ummarsa karshe sun nemi goyan bayan jama’a don karisa abin alherin da yake gudanarwa a fadin karamar hukumar baki daya.

Binciken da jaridar TAURARUWA tayi shine wani sakamako bayar da tallafin maganin zai bayar a halin yanzun?

Binciken ya tabbatar da cewa bayar da tallafin maganin a irin wannan yanayi da ake ciki na wahalar rayuwa zai taimakawa siyasar Dan majalisar ta kowani bangare ganin yadda magani yayi karanci a asibitocin gwamnati kuma yayi cada a asibitocin masu zaman kansu domin a yanzu yin Operation ga mara lafiya ba karamin tashin hankali bane wanda haka yasa da yawa suke rasa ransu bisa rashin kudin maganin ko kudin yin operation din domin komin kankantar operation akan caji kudi mai yawan gaske ne a asibitocin gwamnati Dana yan karuwa.

Bincike ya tabbatar cewa bayar da wannan tallfi da Dan majalisar keyi yana karawa jambiyarsa ta APC farin jini duk da matsin lamba da jambiyar ke sha a wajan mutane.

Shugaban ayarin likitocin dake karkashi ayarin ( Doctor on the move Africa) Dakta Kgbu a jawabinsa ya tabbatar da cewa in Allah yaso zasuyi aikinsu cikin nasara damar za a ci gaba da basu goyan baya kamar yadda aka saba a lokutan baya ya tabbatar da cewa daruruwan mutanene zasu sami operation a bangarori daban daban bayan an gama masu gwaje gwaje da ikon Allah.

Honorabul Injiniya Muhammad Usman shine shugaban karamar hukumar Sabon Gari shi kuma godiya yayi ga Dan majalisar nasa bisa kokari da yakeyi a bagarori da dama yace da yan siyasa za suyi koyi da abin da honorabul Babawo yakeyi to da an sami ci gaba sosai a cikin siyasar kasasu Nigeroya take yayi masa fatan alheri kuma ya nemi goyan bayan jama’a wajan mara masu baya a zabe mai tahowa.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment