Dan majalisa ya baiwa malamai tallafin abin hawa a karamar hukumar sabon Gari

Daga Saiyada Adam,Zariya

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon gari a jihar Kaduna Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo ya mikawa wasu limaman addinin Islama mashina guda 32 kirar BAJaJ don hidimtawa addini.

Wakiliyar mu ta zanta da wasu daga cikinsu a yayin da suke karban kyautar a gidan Dan majalisar dake GRA Sabon Gari jihar Kaduna.

Sheik malam Salisu Umar shine sakataran majalisar malamai na kungiyar Izala ta kasa reshen karamar hukumar Sabon Gari cewa yayi a gaskiya babu wata magana da zanyi face godiya ga Allah saboda irin kokari da Dan majalisar keyi wa addini a fadin karamar hukumar Sabon Gari baki daya.

Sheihin malamin ya kara da cewa da ana samun wakilai irin honorabul Babawo to tuni da mutane sun sami ci gaban rayuwa mai yawa fiye da halin da ake a yanzu.

Sheihin malamin ya kara da cewa su shaidace akan duk aiyukan da Dan majalisar keyi ga jama’arsa a duk bayan wata biyu ko kasa da hakan.
Dan majalisar yakan kaddamar da aikin alheri ga jama’ar karamar hukumar Sabon ta Sabon Gari iri daban daban

Ya zama mutum daya tamkar da dubu a cikin yan siyasar jihar Kaduna da kasa baki daya a cewar sheihin malamin

Domin a binciken da majalisar malamai na Fitiyanu na karamar hukumar Sabon Gari tayi ya zuwa yanzu babu inda Dan majalisar bai tababa a bangaren rayuwar al’umma musamma maganar Ilmi da harkar lafiya da kula da marasa galihu acewar malamin gaskiya yanayi bakin gwargwadon iko kuma gaskya kwalliya na biyan kudin sabulu.

Karshe malamin ya tabbatar da cewa in har Dan majalisar zai tsaya takar sau dubu to zai lashe zabeshi da ikon Allah don haka ake bukata ga duk wani shugaba yayin da yake shugabcin al’ummarsa

Sheik malam Nasir limamin masallacin anguwar Yar Dorawa na daya daga cikin wanda ya shaida da kyautar a wannan lokacin

Liman malam Umar Sambo Alfa limamin masallacin Idi na U PE kallon kura samaru shima ya shaida lamari tare da fatan alheri ga Dan majalisar.

Alhaji Babawo karami shi ya wakilci Dan majalisar yayin raba mashinan ga malaman.

Yayin da Babawo karami yake zantawa da manema labarai ya tabbatar da cewa Dan majalisar ya bayar da mashinanne don taimaka wa addinin Islam tare da neman goyan bayan malaman a takarassa na kujerar majalisar tarayya da ke tahowa kwanaki kadan masu tahowa.
Kuma Dan majalisar ya dau alkawarin in ya sami hasara zai ci gaba da kawo ci gaba a yankinsa fiye da yadda yakeyi a baya .

An fara taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment