Mutum 1000 ne UBA SANI NETWORK FOR PROGRES suka ba tallafin magani a Dan Bushiya da Anguwar KeKe dake kaduna

Daga wakilinmu

A kalla mutane 1000 ne suka sami tallafin magani daga shararriyar kungiyarnan mai suna UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS a yankin Dan Bushiya da Anguwar KeKe dake a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Taron an gudanar dashine a wurare guda 2 na farko a gudanar dashi ne a anguwar Dan Bushiya inda aka tallafawa mutane 500 sai Anguwar Keke inda aka gudanar da shi a LEA Primary Schools nanma an baiwa mutum 500 mutane da yawa ne suka sami halarta taron bayar da tallafin a dukkan bangarori biyun

Alhaji Ahmed Sani shine shugaban wannan kungiya ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS da yake gabatar da jawabinsa yayi kaddamar da tallafin maganin a wannan yankin ya farane da godiya ga Allah tare da nuna jinjina ga al’umar da suka amsa gaiyatar da sukayi masu a wannan lokacin

Shugaban ya sha alwashin ci gaba da irin wannan hidima ga jama’a zarar jama’ar sun bayar da goyon bayansu ga dan takarasu na kujerar gwamnan jihar kaduna a jambiyar APC wato Sanata Uba Sani in Allah ya kaisu lokacin

Karshe yayi matukar farin ciki bisa yadda jama’a suke bin doka da oda yayin bayar da tallafin maganin

Honorabul Muhammad Jalal daga Fiscal Responsibility Commission Kaduna State shine ya zamo shugaban taron a bangaren anguwar Dan Bushiya lokacin bayar da tallafin maganin.

A cikin bayaninsa ya sanyawa taron albarka tare da nuna goyon baya ga kungiyar da fatan alheri ga tafiyar tasu kuma yace in Allah yaso jama’ar wannan yanki zasu ci gaba da samun tagobacin siyasa in suka bayar da goyon baya ga mutane masu manufofi kyautatawa al’umma.

Haka zalika Dakta Christy Ayi Alademerin
Permanent Member ce a Human Resources kaduna SUBEB kuma ita ce shugaban taro kuma wakiliyar mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna a wajan taron.

Itama tayi kyakykyawan jawabi a madadin maitaimakiyar gwamnan na jihar Kaduna Dakta Hadiza Sabuwa Bakarabe.

Har wakiliyar gwamnan tace gwanatin jihar Kaduna zata ci gaba da shareware jama’ar jihar ta hawaye da ikon Allah karshe ta yaba kokarin kungiyar tare da fatan alheri ga dukkan mutanen da suka halacci taron.

Malam Muhammad Ibrahim shi ma ya zamo bubba cikin many an baking da suka shugabanci wannan tarukan bayar da tallafin.

Alhaji Muhammad Ibrahim shima ya nuna farinkikinsa da ganin yadda kungiyar ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS ke gudanar da aikinsu nan take yayi fatan alheri garesu da sauran al’ummar da suka sami damar halattar taron.

Suma bangaren sarakuna da limaman addinai sun sami zuwa wajan taron kuma sun yiwa shugaban kungiyar ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS fatan alheri daya kawo wa jama’ar yankuna biyu Dan Bushiya da anguwar Keke tallafin magani da fatan Allah ya taimaki tafiyar ta Dan takarar kujerar na gwannan jihar Kaduna Sanata Uba Sani insha Allahu.

Abin ban shawa a wajan taron shine yadda sarakuna da malamai suka gudanar da jawabai na nuna jin dadinsu da kokarin kungiyar da ta kawo tallafin dukkansu sunyi fatan alheri ga shugaban kungiya bisa namijin kokarinsa da ya nuna a wannan ranar

Bincike ya tabbatar da cewa a kalla mutun 1000 ne suka amfana da tallafin maganin.

Haka zalika tallafin ya shafi gwaje-gwaje ne a bangarorin da dama tare da bayar da magani bayan tabbatar da irin lalurar dake damun wanda aka gwada.

Malam Nuhu daga anguwar ta Dan Bushiyar na daya daga cikin wanda aka gwada har aka bashi magani shima yayiwa Dan takarar fatan samun nasara a wannan zabe mai zuwa

Ya zuwa hada wannan rahoton mutane da yawa suke sanyawa tafiyar neman nasarar Sanata Uba Sani bisa kokarin da kungiyoyin da ke tare da shi suke yi

An kaddamar cikin tsari an fara cikin tsari.

Leave a comment