Zaria Online Journalist Forum Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Farfesa Idris Abdulkadir

…..Mahaifinmu mutum ne mai hakuri da tawakkali– inji ‘Ya’yan mamacin

Daga Idris Umar,Zariya

A ranar Juma’a 14 ga Afrilun 2023, membobin kungiyar masu wallafa labarai a kafar yanar Gizo da ke garin Zariya cikin jihar Kaduna,(ZOJF) ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir a Zariya.

Tawagar wacce shugaban kungiyar, Ammar Muhammad Rajab ya jagoranta ta je Zariya ne domin ta’aziyyar rasuwar Farfesa Idris Abdulkadir, wanda ya rasu a ranar Litinin, 10 ga Afrilu, 2023.

Daga cikin membobin da suka halarci taron sun hada da wakilai daga kafofin yada labarai na yanar gizo daban-daban wadanda suka hada da; Madogara, Leadership, Noble News, Freedom Rediyo, Dillaliya, Rariya, da Jaridar Daily Struggle.

Tawagar ta samu tarbar dan marigayin na biyu Abdulkadir Idris inda suka yi addu’ar Allah madaukakin Sarki da ya gafarta wa Marigayin, ya kuma sanya shi a Aljannah Firdausi.

Sun kuma yi addu’ar Allah ta’ala ya bai wa iyalan juriyar wannan babban rashi. Sannan kungiyar ta gabatar da takardar ta’aziyya ga iyalan.

A wata tattaunawa da dansa na biyu da ya rasu, Abdulkadir Idris ya jaddada cewa tabbas za su yi kewar mahaifinsu domin shi mutum ne da ya dace a yi koyi da shi; “Shi mutum ne mai adalci kuma mai gaskiya, kuma shi jagora ne wanda a ko da yaushe yake yin adalci ga wadanda ke karkashinsa,” in ji shi.

Tawagar ta kuma ziyarci Farfesa Ango Abdullahi a gidansa da ke Zariya domin yi masa ta’aziyyar rasuwar dan uwansa kuma abokin aikinsa.

Har zuwa rasuwarsa, Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir ya kasance shugaban kwamitin amintattu na kungiyar bunkasa ilimi ta Zariya (ZEDA) mai zaman kanta.

Marigayi Farfesa Abdulkadir ya kasance Farfesa a fannin likitancin dabbobi a Jami’ar ABU Zariya, inda ya rika samun matsayi har ya kai ga zama shugaban tsangayar likitan dabbobi na jami’ar.

An nada shi a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), inda ya dawo da Hedikwatar Hukumar daga Legas zuwa Abuja inda ya yi nasarar gina katafaren ginin da ke kan titin Aguiyi Ironsi, Maitama, a Abuja wanda a yanzu ta zama hedikwatar Hukumar.

Lallai an sanya wa wani dakin taro a hukumar suna ‘Prof Idris Abdulkadir Auditorium’.

Marigayin ya kasance shugaban kwamitin gudanarwa na rusasshiyar kamfanin hada magunguna na Zariya wato ‘Pharmaceutical Company (ZPC) Ltd’, wanda ke kera ‘ZARINJECT’ wato sirinji da allura a Zariya.

Ya kuma kasance Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) dake Kaduna.

Farfesa Idris Abdulkadir ya auri mata 3 inda ya kuma haifi ‘ya’ya gomo 6 maza 4 mata.

Ya zuwa hada wannan rahoton al’ummar zariya da kasa baki daya sai nuna alhinin rasuwan Farfesa Idris Abdulkadir suke.

Leave a comment