Akwai Bukatar Gwamnati Da Mawadata Su Tallafawa Marasa Karfi- Sarkin Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL ya bukaci Gwamnati ta samar da wata hanyar da al’uma zasu samu saukin rayuwa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama.

Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al’amuran rayuwarsu.

Ya kuma tunasar da al’uma shirin gwamnati na Kidayar al’uma da za’a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al’uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar.

Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu’oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikace da gwamnati takeyi tana yin domin al’uma.

Ya godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da ilimi, Noma, Masana’antu da gina tituna da Gadoji inda yace wannan yasa an samu cigaban habaka tattalin arzikin jihar nan da masu saka hannun jari da kuma shigowar masu yawon bude idanu.

Daganan sarkin ya godewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul tareda yi masa addu’a da fatan alheri samun matsayi na gaba sakamakon gabatowar karshen wa’adin mulkinsa.

Da yake Jawabi Mukaddashin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya godewa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR bisa wannan ziyara da yakawo gidan Gwamnati ta Hawan Nassarawa inda yace wannan ziyara ce ta al’ada da aka gada daga wajan magabata.

Dr. Gawuna ya godewa al’umar jihar Kano bisa hadin kai da goyon baya da suka baiwa gwamnatinsu har na tsawon shekara 8 da sukayi suna mulki, Yana mai kira a garesu dasu cigaba da kasancewa masu bin doka da oda a kowanne lokaci.

Leave a comment