Kungiyar tsaffin daliban kwalejin Gwamnati ta yan mata ta Dala sun yi taron cika shekaru 25

Daga Ahmad Suleiman

Kungiyar tsofaffin daliban kwalejin Gwannati ta yan mata ta Dala “GGC Dala” yan aji na 1998 sun gudanar da taron cika shekara 25 da kammala kwalejin.

Taron wanda aka gudanar a dakin taro dake cikin harabar kwalejin ranar Asabar ya sami halartar dinbin tsofaffin daliban da wasu daga malamai da suka koyar da su.

Shugabar kungiyar tsoffin daliban yan aji na 1998.Hajiya Maryam Abubakar Muhammad tace taron na sada zumunci ne a tsakaninsu da kuma karrama malamansu da taimakawa kwalejin ta Dala.

Ta ce wannan haduwa koyi ne da irin tarbiyya da malamansu da iyayen su suka dora su akai na taimakawa juna.Suna bada gudummuwa wajen gyara makaranta da zuwa su koyawa na bayansu dalibai darussa musamman na tsaftar jiki da karfafa musu gwiwa kan dagewa akan neman ilimi.

Ta ce iri n kulawa da malamai suka basu a lokacin suna dalibai gani suke kamar ana takura musu ne,amma yanzu gashi suna cin gajiyar irin tarbiyya da suka basu,mafi yawancinsu sun gama karatu sun zama ma’aikata a fannoni daban-daban da suke amfanar da kansu da al’umma.

Hajiya Maryam Abubakar Muhammad tace sun karrama malamansu 13 da suka koyar dasu tareda yin addu’oi ga wadanda suka rasu daga cikin malaman da kuma yan’uwansu dalibai.

Daya daga cikin malamai da suka koyar da yan aji na 1998 da aka karrama a taron Malam Aminu Musa Sulaiman ya ce shine malami da aka dorawa kulawa da daliban farkon zuwansu makarantar a ajujuwa 12 da adadinsu yakai 400 ya samesu yara ne masu ladabi da biyayya a lokacin.

Ya yi nuni da cewa kammala karatunsu a kwalejin shekaru 25 kenan, sun yi aure sun zama iyaye,da yawa daga cikin su suna ayyuka a ma’aikatu daban-daban wasu na harkokin kasuwanci hakan abin jin dadi ne garesu.

Malam Aminu Musa Sulaiman ya ce a lokacinda tsaffin daliban ke kwalejin sun tarbiyantar dasu akan kyautata dangantaka a tsakaninsu wannan tasa har yanzu suke cigaba da kyakkyawan hulda a tsakaninsu na gina cigabansu dana kwalejin da kulawa da su Kansu malamansu.

Da take zantawa da yan jarida daya daga tsoffin daliban Hajiya Ummi Dauda Raula wacce sakatariyar kungiyar ce ta yan ajin 1998 ta bayyana mutukar jin dadinta bisa taron.Ta yi nuni da cewa kungiyar tasu na taimakawa musamman ga marayu da yan ajin suka rasu suka bari.Sannan suna taimakawa kwalejin da yanzu haka ma sun baiwa kwalejin fartanya 100 da maganin kwari na feshi.

Ummi Dauda Raula tace kungiyar tsoffin daliban na kwalejin yan aji na 1998 da sun jiyo wata matsala nan da nan zasu hadu su dauki mataki su shugabannin kungiyar, sai dai in wani abune da yafi karfinsu sannan zasu nemi daukin sauran yan kungiyar.

Hajiya Mairo Abdullahi na daga cikin shugabanin tsaffin daliban yan ajin shekarar 1998 ta bayyana gansuwar ta da irin hadin-kai da goyon baya da yan kungiyar ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan bunkasa cigaban kungiyar su ta (DOGA)

Leave a comment