JUYIN MULKI A NIJAR: Majalisar Shura Ta Darikar Tijjaniya Ta Nuna Kin Amincewarta Wajen Yin Amfani Da Karfi Soja Domin Warware Matsalar 

.… Tace Yin Amfani Da Difilomasiyya Shine Mafita

Daga Shehu Usman Yahaya

Daga Shehu Usman Yahaya 

Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniya na fadar sarkin Kano ta  nuna kyamarta da kin amincewa wajan yin amfani da karfin Soja, wajan warware Matsalar Kasar Nijar.

Majalisar taba da shawarar a ci gaba  da yin amfani da hanyar Difilomasiyya kasancewar Nijeriyya da Nijar duka abu daya ne. Majalisar ta bayyana haka ne a jawabin bayan taron zikirin juma’a na fadar mai martaba Sarkin Kano wanda aka gudanar ranar juma’a wanda ya samu sanya hannun  shugaba da 

Sakataren kwamitin yada Labarai  Malam Ibrahim Inyas Abubakar da Abubakar Balarabe kofar Naisa .

Hakazalika, taron yayi kira ga al’umar Musulmi su Maida hankali wajan yin Addu’oi domin warwarewar matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassa Kasar nan da kuma tsadar rayuwa da ake ciki yanzu.

” Muna kira ga Hukumomi su tashi tsaye wajan magance matsalolin shaye -shaye ga Matasa, rashin aikinyi da magance ayyukan assha da ake fama dasu daga bangaren Matasa”

” Muna kira ga Gwamnati a kowanne mataki su tallafawa al’umma domin rage radadin halin matsi da al’umar Kasar nan suke ciki”

Taron yayi bayani akan irin yadda sufanci ya bada gudunmawa wajan yada ilimin addinin Musulunci tare da karantar da ingantacciyar fahimtar addinin Musulunci da yada zaman lafiya a tsakanin al’uma.

 Taron yaja hankalin iyaye akan su tsaya ga abunda ya zama wajibi akansu na tarbiyar ‘yayansu da kiyaye lafiyarsu, Mutuncinsu da karesu daga fadawa cikin miyagun ayyuka. 

Haka kuma an bukaci al’umma su koma zuwa ga Allah da yin tuba da kamewa daga barin laifuka wadanda Allah ya hana, kyautata mu’amulla a tsakanin juna, tausayawa na kasa, domin yin hakan Allah zai dubemu da rahamarsa ya yaye mana halin da muke ciki.

Taron ya tsawatar wa masu fassara littattafan magabata da ra’ayin su ba tare da sanin abinda mawallafan suke nufi ba, domin kaucewa batanci ga marubutan da kuma dora Al’umma akan gurbatacciyar fahimta.

 Hakazalika, anyi  kira ga mabiya  Darikar Tijjaniyya su cigaba da aiki da koyarwar Shehu Ahmadu Tijjani (RA) da Shehu Ibrahim Inyass (RA) suka dorasu akai.

Daga  karshe anyi  addu’a ga shugabanni akan Allah yayi ruko da hannayensu yayi musu jagoranci kuma yasa tausayin Al’uma a zukatansu.

Leave a comment