APC za ta dawo da karfinta a Kano- Sanata Barau

Daga Shehu Usman Yahaya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya bayyana cewa yana da karfin gwiwar lallai Jam’iyyar APC za ta dawo da karfinta a Kano, sannan ya bukaci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar da su kasance tsintsiya madaurinki daya.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar Mataimaka Shugabannin Kananan Hukomomi reshen Jihar Kano, inda ya kara da cewa da hadin kai da kuma addu’a, za su samu nasara a Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Gwamnoni.

Jam’iyyar APC na kalubalantar sanar da Abba Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kano wanda aka yi a ranar 18 ga Maris a Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnoni.

“Muna fata kuma muna addu’ar hukuncin da za a yanke mu ne za mu yi nasara. Komai a hannun Allah yake, kuma da yardar Allah lokaci kawai muke jira. Za mu dawo da karfinmu a Kano.

“A yanzu dai mu ne muke adawa, saboda haka akwai abubuwa da dama da ya kamata mu yi. Dole mu hada kanmu domin ciyar da jam’iyyarmu gaba,” inji shi.

Da yake yaba wa mataimaka shugabannin kananan hukomomin bisa ziyarar da suka kawo masa, Sanata Barau ya ce zai cigaba da aiki da su domin inganta rayuwar mutanen jihar.

“Kananan hukumomi na da matukar muhimmanci. Za mu cigaba da aiki da ku domin magance matsalolin da mutanenmu suke fuskanta. Muna alfahari da ku matuka.  Ina fata za mu cibaga da aiki tare,” inji shi.

Tun a farko, da yake jawabi, shugaban kungiyar, Alhaji Yakubu Musa Naira ya ce sun kawo masa ziyarar ce domin su taya shi murnar zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Leave a comment