Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bada Tallafin Karatu Ga Dalibai 200

Shugaban Gidauniyar Tunawa da sardauna Injiniya Abubakar Gambo Umar
Daga Shehu Usman Yahaya

Gidauniyar Tunawa da Sa Ahmadu Bello ta bai wa dalibai 200 masu Karaun digiri tallafin domin samun samar ci gaba da karatunsu daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya.

Shugaban Gidauniyar injiniya Abubakar Gambo Umar, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai jim kadan bayan bude taron bayar da cak ga daliban a Kaduna.

Injiniya Abubakar Gambo Umar ya bayyana cewa tallafin karatu ya kasance ga daliban da ke karatun kimiyya, injiniyanci da kwasa-kwasan likitanci.
A cewarsa, gidauniyar tana zabo daliban da suka kammala karatun digiri na mataki 200, guda 10 daga kowace jiha daga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja domin bayar da tallafin karatu.
Shugabannin Gidauniyar tare da Daliban da suka samu tallafin

A cewarsa "Ana bayar da tallafin ne kawai ga daliban da ba su da hali kuma suke da matsala wajen daidaita kudaden makaranta"

"Muna tabbatar da cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin hazikan dalibai ne wadanda ke da maki 2.5 ( CGP) zuwa sama duka a jami'o'i da kuma kwalejin fasaha."

Shugaban ya kara da cewa an bayar da kyautar ne ga dalibai daga mataki na 200.Ya bayyana cewa, kusan kashi 47 cikin 100 na wadanda suka ci gajiyar shirin sun kammala karatun matakin na farko daga jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha daban-daban na kasar nan.
 “Mun ji dadin cewa mun taba rayuwarsu kuma abin alfahari ne sun zama abin da muke kira Malaman Sa Ahmadu Bello,” inji shi.

Injiniya. Umar ya bayyana cewa gidauniyar ta kasance tana hada kan wadanda suka ci gajiyar shirin domin sanin kansu, da raba gogewa, da kuma shiga cikin shirye-shiryen daban-daban da gidauniyar take shiryawa.

Ya kara da cewa, “Wasu daga cikin wadanda ba su samu aikin yi ba, muna taimaka musu ta hanyar ba da shawara don samun aikin yi a ma’aikatun gwamnati ko kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Yana mai cewa tun bayan kafa gidauniyar a shekarar 2009 da Gwamnonin Arewa 19 suka kafa gidauniyar ta tsunduma cikin harkokin ilimi, kasuwanci, koyan sana’o’i da kiwon lafiya.

“Mun yi ta tsoma baki sosai a kan dabi’un shugabanci, tare da gudanar da laccoci na shekara-shekara kan shugabanci na gari, kuma mun samu nasarori da dama wajen magance rikice-rikice da samar da zaman lafiya a fadin Arewa”.

“Har ila yau, mun yi taka-tsan-tsan kan matsalolin da ke da alaka da ‘yan gudun hijira da ‘yan gudun a fadin Arewa da dai abubuwa da dama da suka shafi ci gaban Arewa.

Leave a comment