TSARO: Nijeriya Tana Bukatar Jami’an Tsaro  Miliyan Takwas Domin Magance Matsalar Tsaron Da Ya Addabi Al’umma – Inji  Dakta Awwal Abdullahi

 **Bamu Amince Da Kalamun Gwamnan Katsina Ba Na Al’umma Su Dauki Bindiga

**  Akwai Bukatar Al’umma Da Jami’an Suyi Aiki Tare Domin Samun Bayanan Sirri

Dakta Awwal Abdullahi Aliyu,  shine shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin ‘Yan Arewa ta kasa wato ” Northern Consensus Movement ” wanda take da kungiyoyi sama da 500 a cikinta daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya waxanda suke magana da murya dada akan lamuran da suka shafi Arewa.

Ya bayyana cewa muddin ana bukatar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi Arewa Sai an samar da hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro wajen bayar da bayanan sirri. Hakazalika,  yace akwai bukatar gwamnati ta kara yawan jami’an tsaron kasar daga miliyan biyu  zuwa miliyan takwas inda yace Nijeriya tana bukatar jami’an tsaro akalla guda miliyan takwas wadanda zasu tunkari matsalar tsaro.

A zantawarsa  da yayi da wakilanmu  Usman Shehu  Yahaya a ofishinsa dake Kaduna, Dakta Awwal Abdullahi Aliyu,  ya nuna rashin amincewarsu dangane da matakin gwamnan jihar Katsina na cewa al’ummar jihar su dauki bindiga domin kare kansu daga harin yan ta’addan da suka addabi jihar. Yace gwamnatin tarayya itace kadai take da hurumin fadawa al’umma cewa su dauki makami ba gwamna ba.

Ga  dai yadda hirar tasu ta kasance:

Gashi yanzu yankin Arewa ya fada cikin marazanar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Shin wadanne irin mataki kuke dauka domin ceto yankin daga cikin wannan halin?

Da farko dai Bari mu dauki matakin tsaro. Duk inda muka ga akwai matsala mukan fito muyi bayani cewa akwai matsalar rashin tsaro a wuri kaza kuma mu aikawa duk hukumomin da suka kamata wato dukkanin jami’an tsaron kasar nan a rubuce duk da cewa mun San sun sani Amma mukan kaddara cewa basu sani ba  Amma mu munsan sun cewa sun sani. 

Duk wani wanda muka San Mai fada aji ne a kasar nan kama daga  shugaban kasa da tsoffin shugabannin kasa da da gwamnoni da kuma majalisar dattawa data wakilai da dai sauran su duk mukan sanar dasu halin da ake ciki sannan mu bada shawarar cewa idan anyi kaza za’a samu mafita.

Bama tsayawa nan sai mu garzaya kafafen yada labarai irin naku mu sanar da al’umma irin halin da Arewa take ciki, wannan kenan domin samo bakin zaren.

Sannan mukan shirya taro mu kira manyan mutane da masana muzo mu zauna mu dubi matsalar tsaron da kanta sannan mu fito da hanyoyin da za’a warware su

Kwanan baya mun shirya wani taron koli ga Fulani wanda muka kira shi da ” Fulbe Fulani Summit” wanda shine irinsa na farko a Nijeriya inda muka tara suk hardodin fulani da suke faxin Nijeriya da kuma sarakunan Fulani da suke kasashen Afirka guda bakwai irin su Ghana da Barkino Fasso Qasar Benin da Mali da kuma qasar Chadi  da Cameron da kasar Sierra Leone, munyi taro dasu a Abuja wanda gwamnonin Arewa guda bakwa da mai Bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro duk sun halarci taron da wakilan shugannin tsaro.

 Mun shirya taron ne domin Gano menene matsalar Fulani kuma wacce hanya za’a bi wajen shawo kan matsalar kuma mun samu bayanai masu inganci akan matsalar. 

Shi Kansa babban bako Mai jawabi tsohon hafsan tsaron Nijeriya Abdulrahman Danbazau, ya fito da gundarin  bayani akan tsaro kama daga matsalar tsaron da wadanda ake ganin sune suke kawo matsalar tsaron wato Fulani da yadda za’a magance matsalolin.  Akan Hakan ne muka cewa Fulani to yanzu fa Kule a gare ku, ya zama wajibi a zauna a ga yadda za’a magance matsalolin da shi Danbazau ya zayyana su kuma bayan taron mun turawa hukumomin tsaron kasar nan harda fadar shugaban kasa akan shawarwarin da aka bada akan yadda za’a magance matsalolin tsaro a Arewa.

Idan muka dawo vangaren tattalin arziki kuma mu abinda muka a sani a Arewa shine noma da kiwo wanda sune abinda aka San dan Arewa dashi kenan. Kamar yadda ka sani dai waccan matsalar ta tsaron itace dai take kara kawo koma baya akan tattalin arziki domin ta Hana manoma suje suyi noman kuma ta hana wadanda ba makiyaya bane kiwon. Noma shine jigon tattalin arziki domin Sai an noma za’a kai kasuwa a sayar haka idan aka kiwata za’a kai kasuwa a sayar Sai gashi wannan matsalolin tsaro ya Hana kasuwancin saboda haka wannan illace babba.  A taron namu kungiyar mu ta fito da matsalar noma da kiwo da ilimi da kuma harkar lafiya wanda duk matsalar tsaron ya cakuxa komai ya Hana gwamnatocin Arewa motsi ita kuma gwamnatin tarayya tace tana bakin kokarin ta su kuma mutane a can qasa suna ganin kamar babu abinda da akeyi.

Kamar yadda nace mu a namu vangaren muna iya bakin kokarin mu wayar da kan al’umma irin hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Arewa.

Dakta Awwal Abdullahi Aliyu tare manyan Jami’an Tsaro Jim kadan bayan wani taro

Gwamnan Jihar Katsina yace lokaci yayi da al’umma zasu xauki bindiga domin kare kansu daga harin ‘Yan ta’adda, shin kana ganin irin wannan matakin zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron?

Gaskiya fisabilillah! Mu bamu yarda da wannan tsarin ba na al’umma su mallaki bindiga ba, idan kace kowa mallaki bindiga kaga ka hada da mutumin kirki Dana banza da wanda zai mallaketa domin kare kansa da wanda zai mallaketa domin kwacewa jama’a halaliyarsu, to kaga akwai matsala babba.

Eh! Na gamsu a matsayin shi na gwamna wanda yayi rantsuwa zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma Yana da wannan fishi da damuwa akan yadda ake mutane ake kwashe dukiyoyin su ake yiwa mata fyade da dai sauransu. Idan  kaji gwamna yayi wannan magana za’a iya Misa uzuri domin wani nauyi ne a matsayin sa na gwamna yake neman ya sauke Amma dokar kasa Bata sahalewa kowanne dan kasa ya mallaki bindiga ba. Tsohon gwamna Katsina Masari Shima yayi irin wannan magana cewa kowanne bakatsine ya mallaki bindiga domin baiwa kansa kariya. Gaskiyar magana shine dokar kasa Bata yarda ba kuma gwamna bashi da hurumin cewa mutane su mallaki bindiga ko makami domin hurumine na gwamnatin tarayya.

Alal misali, gwamna Radda ya kaddamar da ‘yan sa kai wadanda zasu taimakawa jami’an tsaron jihar kuma an basu bindigar harba ka ruga Amma dai Masari shi ya fara aikin. Sai dai mu abin Jin dadi shine wani gwamna ya fara aiki wani wanda ya gaje shi  yaci gaba da shi toh kaga inda za’a ci gaba da irin wannan tsarin a Nijeriya za’a samu ci gaba sosai saboda abu ne mai kyau.

Amma dai  babu wani gwamna da yake da hurumin fadawa al’umma cewa su dauki makami.

Ku ke jagoranta kungiyoyin Arewacin qasar nan, shin me kuke ganin shine mafitar matsalolin da suka shafi Arewa ne musamma tsaro wanda shine yake damun al’ummar yankin a halin yanzu?

Gaskiyar magana shine, abubuwa guda uku suna da matuar muhimmaci a cikin wannan tsarin. Abu na farko shine aiki tsakanin al’umma da jami’an tsaro saboda jami’an tsaro su kadai bazasu iya magance matsalar tsaro ba saboda su ma mutane kamar kowa Sai dai bambamcin horo na dabarun kisa lokacin yaki da suka samu Amma suma mutane ne kamar sauran mutane kuma Sai suna da cikakken bayani na sirri wanda shine zai taimaka musu domin cimma nasara. Misali, Sai ya zama akwai wasu gungun mutane suna taro kuma taron ana kyautata zaton zai iya haifar da matsalar tsaro to Sai a sanar da jami’an tsaro a cikin sirri suzo su kama waxannan mutane cikin sirri, to kaga idan za’a samu bayanai na sirri ga jami’an tsaron zai rage matsalar tsaro matuka saboda haka Sai an samu haxin kai tsakanin al’umma da jami’an muddin ana San magance matsalar.

Abu na biyu kuma muna da karancin jami’an tsaro saboda jami’an tsaro da muke dasu yanzu bazu iya warware matsalolin tsaron da muke fama dashi ba. Aqalla muna da mutane a Nijeriya sama da miliyan 200 sannan idan ka hada dukkanin jami’an tsaron Nijeriya basu kai miliyan biyu ba to kaga kenan akwai matsala.

Ya kamata ace jami’an ‘Yan Sanda kawai muna da miliyan uku da wani abu ne soja miliyan biyu; DSS miliyan biyu; jami’an fasa kwauri Dana shige da fice miliyan daya-dada Sai ya zama idan ka dunkule su dukka basu miliyan biyu ba ai kuwa akwai matsala sosai akan harkokin tsaro.

Muna kira ga gwamnati ta Bawa matsa dama a xaukesu ayyukan tsaro kuma a dauke su da yawa. Kuma a basu kayan aiki na zamani da Kuma inganta rayuwarsu saboda suna da iyalai zasu biya kudin makaranta da lafiyarsu da sauran buqatunsu na yau da kullum. Kaga dole a kyautatawa rayuwarsu Shima zai taimaka matukar gaske.

Dakta Awwal Abdullahi Aliyu Yana jawabi a wurin wani Taro

Toh! Menene saqonka ga al’ummar Arewa baki daya?

Na farko dai ya zama wajibi ga daukacin matasan Arewacin Nijeriya su zama masu bin doka da umarni; a kaucewa savawa dokar qasa saboda dokar kasa ba karya bace haka kuma ayi biyayya ga shugabanni da yi musu addua Amma ba tsinuwa ba domin a lokacin da ka yi musu tsinuwa zai iya dawo kanka ba Wai kawai kan shugabannin zai tsaya ba. Muna kira ga jagororin Arewa musamma ma wadanda al’umma suka zava su sani cewa akwai hakkin al’umma akansu wanda Allah zai tambaye su na kare dukiyoyin al’umma da rayuwarsu a duk inda suka samu kansu.

Leave a comment