Daga Shehu Yahaya
Jigo a Jam’iyyar APC ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni yake tallafawa kaukacin al’ummar jihar ta bangarori daban-daban a fadin jihar.
Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Alhaji Yusuf Musa, a zantawarsa da manema labarai a Kaduna Jim kadan bayan kungiyar ‘Yan Jarida ta Arewa ta karramashi da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar Yobe da Arewacin Nijeriya baki daya.
Alhaji Yusuf Musa, wanda Yana daga cikin ‘ Yan kwamitin rabon tallafin kayan cire tallafin man fetur na jihar, yace gwamnatin Mai Mala Buni budaddiyar gwamnati ce da kowa zai shaida.
Alhaji Yusuf, wanda shine shugaban kamfanin Yusufana, yace gwamnatin Yabe ta Bawa bangaren lafiya da na ilimi muhimmanci sosai, sannan ta samar da ruwan sha da karfafa wa mata da matasa, domin duk matsalar jihar ya san yadda zai magance ta.
“Gwamnatin Mai Mala Buni tana tallafawa matasa mata da maza domin ana basu kaso mai tsoka. Sannan iyaye mata da suke cikin gida ana taimaka musu wajen samar musu da kananan sana’o’i da za su dogara da su,” inji sh
Shugaban yace a bangaren tsaro, yayi dukan mai yiwuwa wajen ganin ya sake daidaita sha’anin tsaron ya kuma bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Akan Hakan ya yaba da kokarin kafafen lada labarai bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen wayar da kan al’umma akan lamuran yau da kullum. Ya kuma godewa qungiyar ‘Yan jarida ta Arewa da suka karramashi bisa gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa rayuwar al’umma baki daya.