Akwai Bukatar Gwamnati Ta Rika Bawa Kwararrun Injiniyoyi Aiki- Injiniya Ma’aruf Isyaku

 

Injiniya Ma’aruf Isyaku

Daga Shehu Yahaya 

Injiniyoyi a jihar Kaduna, sun bukaci gwamnatoci da su rika amfani da kamfanonin cikin gida wajen aiwatar da ayyukan su wanda hakan zai taimaka wajen kara bunkasa ci gaba a kasa.

Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Babban manajan kamfanin Nalado ( NALADO NIGERIA LIMITED) ,Injiniya Ma’aruf Isyaku, a zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron cikar shekara 50 da kafuwar kungiyar injiyoyi ta kasa reshen jihar Kaduna, wanda ya gudana a dakin taro Na gida Sardauna.

Manajan ya kara da cewa gwamnati tana bukatar kwararrun injiniyoyi domin aiwatar da ayyukan ta, a cewarsa,  Bawa injiniyoyi wanda suke da kwarewa Yana da matukat alfanu  

Injiniya Ma’aruf, yace akwai bukatar gwamnati ta rinka aiki kafada da kafada da kungiyar Injiniyoyi wanda hakan zai nuna cewaa injiniyoyi suna da rawar takawa wajen ciyar da kasa gaba.

Yace ” Wannan taro Yana da matukat muhimmaci saboda shekaru 50 da kafuwar wannan kungiyar a kaduna haka Yana nuna cewa kungiyar tana karfi sosai saboda haka akwai bukatar gwamnati ta rika aiki da wannan kungiya akan duk ayyukan su na yau da kullum, maganar gaskiya akwai wasu abubuwa a gwamnatance ba’a tuntubar injiniyoyi  saboda akwai ayyukan da ya kamata a ba injiniyoyi Sai a Bawa wadanda ba injiniyoyi bane, muna fatan gwamnati zata rinka Bawa injiniyoyi na gida  ayyuka domin samun ingattatun ayyuka” inji shi.

Injiniya Ma’aruf Isyaku,  ya bayyana murna da cikar kungiyar Injiniyoyi ta jihar shekaru 50 da kafuwa inda hakan Yana nuna cewa injiniyoyi a jihar Kaduna suna da karfi.

Daga bisani ya bayar da gudummawar kudi Naira dubu dari a madadin kamfanonin da y wakilta  a wurin taron.

Leave a comment