Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Bayyana Kudirinta Na Hukunta Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Doka  Ba

..Mun Fara Kama Tsoffin Jami’an Tsaro Da ‘Yan Kasar Sin– Dakta Nura

Dakta Mohammed Nura Sani Hussaini Shugaban Kamfanin Bunkasa Ma’adanai na jihar Kaduna

Daga Shehu Yahaya

Gwamnatin jihar Kaduna Jihar Kaduna ta bayyana kurinta na hukunta duk wanda ta samu Yana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar kabi daya.

Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin bunkasa ma’adanai na jihar Kaduna Alhaji Mohammed Nura Sani Hussaini,  a wata zantawa da yayi da wakilanmu.

Shugaban yace tuni suka fara kama masu hakar ma’adanai a jihar ba bisa qa’idaba wadanda suka hada da tsoffin jami’an tsaron kasar da wasu daga Sin  wadanda aka mika su hannun jami’an tsaro domin gurfanar dasu a gaban kotu.

Yace gwamnatin jihar Kaduna tana bakin q

kokarinta wajen dakile masu haqar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta hanya zama da sarakuna da hakimai da dagatai domin nuna musu illar hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma sanar da su irin da yake yiwa rayuwarsu da tattalin arziki jihar.

” Wuraren da ake hakar ma’adanai da bisa doka ba zaka tarar da cewa wurin matattarace ta ‘Yan shaye-shaye  da masu aikata laifuka, saboda haka muna Jan hankalin iyaye da da su daina tura yaransu wurin da ake hakar ma’adanai ba bisa doka domin kula da tarbiyyarsu. Alal misali duk yaran da ya saba samun kuxi 1,500 a kullum ta Yaya zai iya zuwa makaranta? Babu saboda Yarone ya iya hakar kuza ko gwal kuma ya wanke shi ya kai a bashi 1,500 zuwa sama kaga babu yadda za’a yi juya shi. Shi yasa muke ziyartar irin wadannan wuraren domin wayar musu da kai akan illar hakan”

Dakta Mohammed Nura Sani Hussaini, ya ci gaba da cewa  jihar na da albakatun ma’adana masu dinbin yawa kuma jihar ta kasance a kan gaba a bangaren mallakar ma’adanai a cikin jihohin kasar nan.

Ya kara da cewa, an yi fiye da shekara 100 ana harkokin hakar ma’adanbin Gwal a yankin Birnin Gwari. Ya ce, ana hakar ma’adin karfe a yankin kudancin Kaduna, Kubau da Lere.

Ya ce, jihar ta hada hannu da wasu kamfanonin hakar ma’adanai na kasashen waje inda suka zuba jarin fiye da Dala miliyan 600 don kafa kamfanin hakar ma’anin karfe a karamar hukumar Kagarko.

Ya kara da cewa, jihar na a kan gaba a harkar ma’adanin ‘Lithium’ inda suka hada hannun da wani kamfanin kasar Sin a don hakar ma’adanin a kauyen Kangimi da kuma wani hadin gwiwar da kasar Australian a hakar ma’adanin ‘Jubita’.

Dakta Nura ya ci gaba da cewa a halin yanzu Jihar Kaduna ta zama kan gaba a harkokin hakar ma’adanin “Gemstones’ da “Safayers” ana kuma shirin ganin gwamnati ta zuba jari don ganin al’ummun yankin sun amfana yadda ya kamata.

A cewarsa “Jihar Kaduna ta shirya tsaf don samar da hanyoyin amfana daga ma’adanai masu muhimmanci da Allah ya albarkaci jiharmu da su, kamar ‘Amethyst a yankin Ikara, da “Lithium, a yankin Kurega da Manini. Haka kuma kamfanonin qasar Hong Kong sun shigo don hada hannun da mu a bangaren hakar ma’adanin “Tin mining’ a garin Gidan Waya da ke karamar hukumar Jema’a.” 

Da yake bayani akan matakan da suke bi na wayar da kan matasa masu hakar ma’adanaiba bisa doka ba yace ” Gwamnatin Kaduna mai tausayaci, saboda haka ne muka tattara kananan masu haqar ma’adanai wuri guda muka yi musu rigista domin gwamnati ta San da zaman su kuma muka bash horaswa akan yadda ake hakar ma’adanai da yadda zasu kula da lafiyarsu da muhalli  sannan aka basu kayan da zasu rinka Saya irin su takalma da dai sauran abubuwan da zasu taimaka musu”

“Saboda haka gwamnati tana daukar matakan gaske, muna kara kira ga jama’a da su sani kowanne abu Yana da matakai da ake abi akan duk wanda yake so ya fara hakar ma’adanai a jihar kaduna Sai ya tabbatar da cewa ya samo wurin da babu lasisi Sai ya gabatar da kansa da kamfaninshi a matsayin wanda zai fara haqar ma’adanai sannan Sai a bashi lasisi. Ko da an baka lasisi kamin ka fara aikin Sai ka dawo wurin gwamnati taje ta duba wurin hukuma ta duba domin kamin kafa kai kaya Sai an sanar da mai gari da jami’an tsaro saboda mutum baya shiga daji kawai ya fara aiki ba” inji shi

Leave a comment