Masu Lalurar Sikila Na Bukatar Karin Kulawa Lokacin Hunturu – Hajiya Badiyya

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa

Shugabar Cibiyar Tallafawa masu Lalurar Amosanin Jini wanda akafi da Sikila dake jihar Kaduna, Hajiya Badiyya Magaji Inuwa tayi kira ga gwamnatoci da sauran masu hannu da shuni da su sa hannu wajen taimakon masu fama da lalurar sikila musamman a wannan lokaci na hunturu da ake ciki domin saukaka musu halin damuwa da suke ciki.

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa ta yi wannan kiran a yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishin Cibiyar dake garin Kaduna.

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa ta ƙara da cewa maau fama da lalurar Sikila suna shiga cikin wani mawuyacin halin na tagayyara musamman ba lokacin sanyin hunturu wanda ke kara tayar musu da ciwon, inda ta bayyana muhimmancin ɗaukar matakan da suka dace na magance hakan.

“A duk lokacin da muka shigo cikin irin wannan yanayi na sanyi na kan tashi da kaina na tafi kasuwar ‘yan gwanjo a kwance dila a gabana na zaɓo kayayyakin sanyi na zo dasu a rarraba wa masu fama da lalurar”.

Badiyya Magaji Inuwa ta shawarci gwamnati da daukar matakan wayar da kan jama’a akan cutar ta kafafen yaɗa labarai domin sakon ya kai ga inda ake bukata, inda ta koka da yadda masu fama da lalurar ke ƙaruwa lamarin da ta bayyana da karancin wayar wa jama’a kai.

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa ta kuma yi kira ga samari da ‘yan Mata da su tabbatar sun yi gwaji domin sanin matsayinsu kafin aure, inda ta bayyana cewa matukar aka samu cikin jinin da alamun cutar to ya zama dole a dakatar da wannan alaƙa.

Daga ƙarshe Badiyya Magaji Inuwa ta ƙalubalanci limamai da Pastoci akan dakatar da duk wani daurin aure da ya zo gabsnsu wanda ba ya da shaidar yin gwajin jini

Leave a comment