KADUNA: Taron Sulhu Na  NURTW Ya Tashi Baram- Baram

...Ba Zamu Amince Da Yin Karan Tsaye Ga Kundin mulkin Kungiya Ba- Inji  ‘Yan Takara

Aliyu Tanimu Zariya

Daga Shehu Yahaya 

A yayin da kungiyar direbobi ta kasa rashen jihar Kaduna NURTW ta gudanar da taron sulhu a tsakanin mambobin kungiya domin lalubo hanyar da za’a gudanar da zaben kungiyar cikin lumana.

Sai dai taron ya tashi cikin rudani bisa abinda wasu mambobin suka bayyana da rashin adalci da yin Karen tsaye ga kundin mulkin kungiyar. 

Taron wanda ya samu halarcin shugabannin kungiyar na jiha dana reshe da kuma ‘Yan takara wanda aka gudanar dashi a dakin taron kungiyar dake kaduna bisa jagorancin Shugabanta Aliyu Tanimu Zariya.

Bidiyon yadda taron ya kasance

Rahotanni sun ruwaito cewa a yayin taron an rabawa mahalarta taron wata takarda da su sanya sunayensu  a cikinta, ana cikin haka ne sai wasu  mambobin masu neman takara  suka bayyana cewa basu  amince da takardar ba bisa abin da suka kira yaudara da zagon kasa.

Wadanda suka zanta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron sun bayyana cewa takardar an samar da itace domin yin amfani da ita wajen kin gudanar da zaben kungiyar wanda zai gudana cikin wannan watan.

Da yawan wadanda suka zanta da manema labarai sun zargi shugaban kungiyar Aliyu Tanimu Zariya, da yin Karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kungiyar na karbar-karba , da gudanar da mulkin kama karya, inda suka duk wanda ya soki lamarin shugabancin shi Sai ya dakatar dashi daga kungiyar lamarin da suka ce suna neman dauki daga gwamnati da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a kungiyar. 

Idris Mohammed, shine shugaban bangaren motocin Bas masu zirga-zirga a cikin gari reshen Tashar Kawo, ya zargi shugabannin kungiyar da yin kama karya wajen tunanin kakaba musu ‘Yan takara.

Yace ” maganar gaskiya taro ya tashi baram-baram saboda muna cikin taro aka kawo mana takarda fara akace duk wanda yazo da mutanan shi yaje ya rubuta sunansu haka y sanya duk muka je muka sa hannun mu Sai wasu suka Ankarar damu cewa Anya wannan babu matsala kuwa Sai da muka shigo dakin taron Sai aka fara cewa an wannan shine kudirin da aka tsara  acan baya ne. Mu kuma mun San cewa akwai wadanda da dama basu cancanta a kan kujerar ba Sai muka ce a kowa kowanne shiyya a gudanar da zabe yadda ya kamata, saboda muka ce bamu amince da ita wannan takarda ba saboda sunce ita wannan takarda ta ta-zarcen shugabanninda suke kai ne , shine yasa da yawanmu muka ce bamaso bukatar mu shine a koma shiyyoyin kungiyar a gudanar da zaben kungiyar kamar yadda aka saba”

Idris Mohammed,  ya bukaci gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaron juhar Kaduna da su tabbatar da cewa sun shigo cikin harkar kungiyar domin tabbatar da zaman lafiya a cikin NURTW, wanda hakan shine zai kawo ci gaban kungiyar. 

Akan Hakan,  Idris Mohammed yace suna kira ga masu da tsaki a cikin kungiyar da tabbatar da cewa an aiwatar da mulkin karba-karba kamar yadda aka tsara tun farko wanda karbar-karbar itace ta kawo Aliyu Tanimu Zariya kan shugabancin kungiyar.

Rikicin Shugabanci Yana neman raba kan kungiyar ta NURTW reshen Jihar Kaduna wanda tuni aka fara musayar kalamai tsakanin bangaren tsohon shugaban kungiyar Haruna Alhassan 313 da Bangaren shugaban kungiyar Aliyu Tanimu Zariya.

Leave a comment