Daga Shehu Yahaya
Majalisar dattawa ta amince zata gayyaci Shugaban Bankin Manoma ta Nijeriya Alwan Ali Alhassan da ya bayyana a gaban kwamitin Kula da yaki da cin hanci da rashawa domin amsa tambayoyi akan badakalar kudaden manoma.
‘Yan majalisar Datawan sun cimma daukar wannan mataki ne a yayin zamansu da Shugaban Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ( Anti Corruption Corps) Dakta Maina Abdullah Gimba a Abuja.
A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna mai dauke da sa hannun Darakta Janar Ma kungiyar ta ACC Dakta Maina Abdullah Gimba, yace kungiyarsu ta zauna da sakataran kwamitin majalisar Dattawa akan amsar koken al’umma inda suka amince zasu gayyaci Shugaban Bankin Manoman bisa korafe- korafe na karkatar da kudin manoma sama da biliyan 10.
Dakta Maina Abdullah Gimba, ya kara da cewa kungiyarsu ta bankado badakalar kudi na manoma da bankin bisa jagorancin Shugabanta Alwan Ali Alhassan yayi lamarin da ya Sanya suka kai kararsu zuwa majalisar domin gudanar da bincike da kuma daukar matakan da suka dace akan lamarin.
Akan Hakan sun bukaci bayan kammala binciken da ‘yan majalisar, gwamnati ta tsige shugaban bankin manoman wanda a cewarsa, suna da tabbacin cewa an karkatar da kudadan manoman kasar nan.
A zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho, Barista Kaka Lawan Shehu, ya tabbatar da cewa zasu gayyaci Shugaban bankin manoman domin ya kara gurfana a gaban kwamitin Karo na biyu domin amsa zarge- zargen da ake masa akan kudadan manoman Nijeriya.