Zakka Hakkin Talaka Ne Allah Ya Ba Masu Kudi-  inji  Shugaban  Gidauniyar Zakka

Malam Abdullahi Salisu Halidu, Shugaban Gidauniyar Zakka da Wakafi Mai Zaman Kanta Ta Jihar Kaduna

Daga Shehu Yahaya

 Shugaban Gidauniyar Zakka da Wakafi  Mai Zaman kanta ta jihar Kaduna  Malam Abdullahi Salisu Halidu, ya bayyana cewa fitar da zakka wajibi ne ga masu hannu da shuni wanda hakan zai taimaka wajen ragewa al’umma radadin rayuwa da ake ciki a yanzu.

Malam Abdullahi Halidu, ya bayyana haka ne  a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala musabakar karatun Alkur’ani na jihar Kaduna, inda yace fitar da zakka hakkin talaka ne Allah  ya dorawa masu hannu da shuni.

Yace fitar da zakka abu ne wanda ya zama wajibi akan masu hannu da shuni, bisa muhimmancin ta a wurin Allah, a cewarsa, ya zama wajibi ga masu hannu da shuni da su Bawa talakawa hakkinsu da Allah ya basu ajiya.

” Harkar zakka  tana daga cikin shika-shikai na addinin musulunci saboda Allah ya  ambaceta a wurare 30 a cikin Alkur’anai  daga ciki  wuri 27 aka hada ta da sallah wato aka hada muhimmancinta da sallah  kuma shi Allah SWT ya wajabtawa masu hannu da shuni idan kudinsu ya kai wani adadi ko kaso su ba mutane wanda itace kadai hanyar da zamu bi wajen kaucewa wannan radadin rayuwa da ake ciki”

” Ina kira ga masu hannu da shuni  da su sani cewa Ita zakka hakkin talaka ne Allah ya bada a hannunsu saboda haka suji tsoron Allah su cire wannan hakkin su ba talaka hakkinsa. Lokacin Manzo SAW itace  kadai akace idan baka bada ba a kwata da karfi, saboda haka zakka hakkin talaka ne masu kudi su ciro su ba talakawa hakkinsu” inji shi

Akan Hakan,  shugaban ya yaba da kokarin gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani  bisa tallawa harka musabakar karatun Alkur’ani na Bana inda yace ” Shi karatun Alkur’ani Yana kara taimakawa mutane su gyara imaninsu saboda haka taro irin wannan Yana da matukar alfani ga rayuwar al’umma musulmi.

Leave a comment