Gwamnatin Jihar Kano Zata Samar Da Ranar Zakka Da Wakafi

 

Daga Shehu Yahaya

Bisa ganin yadda fitar da zakka da wakafi suke da muhimmaci da daraja a cikin addinin musulunci, Gwamnatin jihar Kaduna zata samar da ranar Zakka da Wakafi wacce akayi nata lakabi da ” Zakka Day”

Mukaddashin Shugaban  Hukumar Zakka da Wakafi na jihar Kano, Yunusa Haruna, shine ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron Kungiyoyin Zakka da Wakafi ta Nijeriy, wanda ya gudana a jihar Jigawa

Shugaban,  yace  gwamnatin Kano, ta kammala shirinta na na sanya ranar da zakka da wakafi wanda za’a rinka gudanar duk shekara-shekara wanda gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da daukacin  kwamishinoninsa da manyan ‘Yan kasuwa da su  za’a kaddamar da ranar.

Sakataren ya kara da cewa hukumarsu ta himmatu wajen samar da hanyoyin da zasu rinka bi wajen karba da raba zakka a fadin jihar baki daya.

Akan Hakan, ya bukaci daukacin masu hannu da shuni da Bawa hukumarsu goyon baya wajen fitar da zakka wanda za’a rabawa mabukata kamar yadda addini musulunci ya tsara.

Da yake bayani dangane da yadda taron AZAWON na Bana ya gudana, ya jinjinawa shugabannin kungiyar wajen shirya taron inda yace taron ya kayarta musamman ganin yadda aka tara masana daga jihohin daban-daban a fadin kasar nan domin tattauna batun zakka da wakafi a Nijeriya. 

Leave a comment