Zakka Da Wakafi Sune Hanyar Yakar Talauci Da Yunwa A Nijeriya- Mai Doki

Daga Shehu Yahaya

Kungiyoyi Masu Aikin Zakka Da Wakafi Ta Nijeriya (AZAWON),  ta bayyana cewa zakka da wakafi sune  hanyar yakar Talauci da Yunwa  a Nijeriya.

Bayanin Hakan ya fito daga bakin Shugaban Kungiyar Na kasa  Malam  Muhammad Lawal Mai Doki ( Sadaukin Sokoto) a yayin da yake jawabi a taron  kali na Kungiyoyin Zakka da Wakafi na Nijeriya karo na uku wanda ya gudana a Dutse babban birnin Jihar Jigawa.

Lawal Mai Doki, yace  rashin fitar da zakka Yana jefa al’umma cikin mawuyacin halin rayuwa da kuma durkushewar tattalin arzikin kasa Baku daya.

Mai Doki, wanda kuma shine mataimakin Sakatare na Kungiyoyin Zakka da Wakafi ta Duniya, ya ci gaba da cewa matukar al’umma za su ci gaba da riko da bayar da Zakka kamar ysdda addinin Musulunci ya tanada babu shakka an samo mabudi wanda zai magance dukkanin wata matsala a kasar nan.

Ya bada misali da halin da ƙasa ta tsinci kanta a ciki yanzu inda Talaka ke wayyo Allah da cewar Zakka ce kadai za ta warware matsalar matukar an fitar da ita yadda ya kamata da kuma bayar da ita ga wadanda suka cancanta.

Taron gamayyar kungiyoyin Zakka da Wakafin na kwanaki biyu na ci gaba da gudana a babban dakin taro na Man Power dake garin Dutse jihar Jigawa kuma ya samu halartar dukkanin ‘ya’yan kungiyar a faɗin tarayyar Najeriya.

Akan Hakan ya bukaci gwamnatoci da su jajirce wajen bunkasa hukumomin bayar da zakka na jihohinsu.

Shugaban ya kuma bayyana gamsuwarsa dangane da irin gudummawa da gwamnatin jihar Jigawa ta Bawa Kungiyarsu wajen daukar bakuncin taron, inda yace akwai bukatar gwamnatin jihar da ta kara  inganta kwamitocin zakka da wakafi na masarautun jihar domin ganin shirin karbar zakka da raba shi Yana tafiya yadda ya kamata.

Leave a comment