Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkin Arewa (NCM) Ta Ziyarci Kauyen Tudun Biri Tare Da Shan Alwashin Ganin Adalci Ya Tabbata

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Gamayyar Kungiyoyin dake rajin kare hakkin Arewa wato Northern Consensus Movement (NCM) a turance ta ziyarci kauyen tudun biri na ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna domin jajanta al’ummar yankin iftila’in da ya faru na harin bom da sojin Najeriya suka kai bisa kuskure a kwanakin baya.

Shugaban gamayyar kungiyoyin na ƙasa Kwamared Awwal Abdullahi Aliyu wanda ya jagoranci kungiyoyin ya bayyana hatsarin da ya faru a matsayin abin bakin ciki da takaici da ba za a manta dashi ba.

Shugaban gamayyar kungiyoyin yace za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an yi wa jama’ar yankin adalci na asarar dimbin rayuka da suka yi a yayin harin sojojin.

Kwamared Awwal Abdullahi Aliyu ya kuma yaba matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka tare da yaba kokarin ƙaramin ministan tsaro da shugaban majalisar dattawa da dukkanin jama’a da suka nuna tausayawa gami da bayar da agaji da taimako ga waɗanda harin ya rutsa da su.

Leave a comment