Gwamnonin Arewa Sun Bada Tallafin  Naira Miliyan 180  Ga Al’ummar Tudun biri 

Daga Shehu Yahaya

Kungiyar Gwamnonin Arewa  19 Sun Tallafawa Wadanda Harin Bam na Tudun Biri a karamar Hukumar Igabi dake jihar Kaduna da kudi Naira miliyan 180 a matsayin  gudummawa domin rage musu radadin asarar da sukayi.

Shugaban kungiyar gwamnonin Muhammadu Inuwa Yahaya, shine ya sanar da hakan a jawabin bayan taron kungiyar tayi a Kaduna yau Juma’a a fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Mohammad Inuwa Yahaya, wanda shine gwamnan jihar Gombe, ya jajantawa gwamnatin jihar Kaduna da daukacin al’ummar Tudun Biri bisa iftila’in da ya samesu a kwanan baya.

Hakazalika,  kungiyar ta bukaci da a gudanar da bincike mai tsauri domin kaucewa farun irin wanan harin nan gaba, tare da hukunta wadanda suke da hannu wajen kai harin.

Kungiyar ta kuma yaba da kokarin gwamnatin tarayya Dana jihar Kaduna bisa daukar matakan gaggauwa wajen tallafawa waxanda suka jikkata da yunkurin kula da al’ummar Tudun Biri. 

Gwamnonin Sun kuma koka dangane da yadda matsalar rashin tsaro yake ta’azzara a yankin Arewacin kasar nan, suna mai daukar alwashin kawo karshen matsalar sace mutane da na ‘Yan bindiga a yankin.

Akan Hakan kungiyar tayi alkawarin tallafawa rayuwar matasa ta  hanyar samar musu da aikin wanda hakan Yana daga cikin matakan da suke dauka na yaqar talauci da matsalar rashin tsaro a fadin yankin baki daya.

Leave a comment