Matsalar Tsaro: Mun Gamsu Da Irin Matakan Da Gwamnatin Zamfara Take Dauka- Gwamna Inuwa Yahaya

Gwamnonin Arewa sun bayyana gamsuwarsu dangane da matakan da gwamnonin Zamfara da Katsina suke dauka domin shawo kan matsalar tsaron da ya qddabi jihohin.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Alhaji Mohammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a jawabin bayan  taron kungiyar da ya gudana a ranar Talata a gidan gwamnati a Kaduna.

Gwamna Dauda Lawal a Taron kungiyar Gwamnonin Arewa

Yace ” Mun gamsu da irin matakan da gwamnonin Zamfara da Katsina suke dauka mataku domin magance matsalar tsaro , bisa irin bayanan da suka gabatar mana nun jinjina misu matuka Wanda Hakan yake nuna cewa akwai alanun nasara”

Da yake bayani dangane da irin matakan da kungiyarsu take dauka domin shawo kan matsalolin da suka dabai- Baye Arewacin kasar Nan ,Alhaji Yahaya ya ce, gina dan Adam na da matukar muhimmanci ga ci gaban yankin, inda ya koka da cewa, a halin yanzu, Arewacin Nijeriya ne ke da mafi yawancin yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.

Gwamnan ya bayyana hakan da dewa, sam bai dace ba kuma dole ne a yi gaggawar magance wannan matsala, wanda ya ce, kowane yaro ya cancanci samun ingantaccen ilimi da kuma damar bunkasa fasahar da ake bukata don samun nasara.

Ya kara da cewa, bangaren tsaro yana kan gaba a abubuwan da kungiyar ta fifita, yana mai jaddada cewa, a taron da suka yi na karshe, kungiyar ta jaddada aniyarta na yin aiki tare da gwamnatin tarayya, domin samar da mafita mai dorewa kan kalubalen tsaro dake addabar yankin.

Leave a comment