Ilimi A Kaduna: Ana Zargin Shugabar Makaranta Da Karbar Kudi Wurin Dalibai

A kokarin da gwamnatin jihar kaduna takeyi  na bayar da ilimi kyauta daga matakin firamare zuwa karamar sakandare, rahotanni sun tabbatar da cewa shugabar makarantar mata dake unguwar mu’azu a karamar hukumar kaduna ta kudu Hajiya Adama Wada, na karbar kudin makaranta a hannu dalibai duk da cewa gwamnati ta haramta haka. 
Iyayen dalibai sun bayyana takaicinsu dangane da yadda Adama Wada take amsar naira dubu uku ga duk dalibar da zata shiga makarantar inda sukayi kira ga gwamnan jihar da waiwai makarantar domin kawo musu dauki.

Makarantar wacce akafi sani da suna  “Day Bola” sashin kananan dalibai, shugaban makarantar ta dade tana karbar kudin iyaye na shiga makarantar da kuma kudin sayan alli na rubutu da dai sauransu.

Iyayen da suka zanta da wakilinmu, sun bayyana shugaban makarantar a matsayin mai yiwa gwamantin kaduna zagon kasa akan harkar ilimi wanda suna neman gudummawar gwamnatin.

Leave a comment