Ina Koyi Da Gwamna El-Rufa’i Ne… Ladi Yahuza


Shugabar riko ta karamar Hukumar Chikun Hajiya Hadiza Ladi Yahuza, ta bayyana kudirinta na inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar ta hanyar bunkasa harkokin ilimi da samar da sana’oi ga matasa maza da mata domin dogaro da kansu kamar yadda gwamnan jihar kaduna malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, yakeyi  a fadin jihar baki daya.

Hajiya Ladi YahuZa, ta bayyana haka ne a yayin da take kaddamar da dakin koyon sana’oi da dakin karatun koyon ilimin kwamfuta wanda ta gina a cikin harabar sakatariyar karamar hukumar dake Kujama,domin amfanar daukacin al’ummar karamar hukumar.

Shugabar ta kuma kaddamar da wani dakin rubuta jarabawa da ta gina a makarantar sakandare dake garin Kujama. Tace duk irin wadannan ayyuka da take yi tana koyi ne da gwamnan jihar kaduna wanda a cewarta, burinsa shine ya iganta rayuwar al’ummar jihar kaduna.

Ta kuma bayyana goyon bayanta da jinjina ga gwamna El-Rufa’i, bisa damar da ya bata na zama shugabar karamar hukuma wanda hakan ya bata damar aiwatar da ayyukan ci gaban jama’ar karamar hukumar.

A jawabansu daban-daban a wurin taron, mahalarta taron sun godewa Hajiya Ladi Yahuza, bisa ayyukan da ta kawo musu karamar hukumar wanda sukace basu saba ganin irin haka sai lokacin Ladi Yahuza, inda suka yi mata fatan alheri.

Leave a comment