COMMONWEALTH: Ta Nada Ngozi Okonjo Iweala A Matsayin Babbar Sakatariyar Kungiyar

Kungiyar kasashen rainon ingila, “Commonwealth” ta nada tsohuwar ministar kudi ta Nijeriya Misis Ngozi Okonjo Iweala, a matsayin babban jami’a a sakatariyar kungiyar.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da Kakakin kungiyar Ferfesa Ben Maloney ya fitar tare da sanya hannu.
Sanarwar ta ce, an zabe ta ne sakamakon cancanta ta, bisa la’akari da gudunmowar da ta bayar a lokacin mulki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Sanarwar ta kara da cewa, tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Kiribati Mista Anote Tong ne ya jagoranci matsayin tun daga shekara ta 2003 zuwa 2016.
Kungiyar ta ce tuni dai ta kaddamar da wani kwamiti da zai fara bibiyar wadda za ta zama sarauniya a kungiyar

Leave a comment