Hukumar NAHCON Zata Mayar Wa Maniyyata Da Basu Sami Damar Zuwa A Hajjin Bara BaNaira Miliyan Dubu Dari Takwas Da Ashirin

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce, ta ware Naira miliyan dubu dari takwas da Ashirin, a matsayin kudaden da za a mayarwa maniyata da basu samu damar zuwa aikin hajjin shekara ta 2017 ba.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin hukumar Malam Adamu Abdullahi ya fitar.
Sanarwar ta ce, daga cikin kudaden akwai Naira dubu dari da takwas da daya da Naira miliyan dubu dari biyu da tara, wanda ma’aikatar lura da aikin hajji ta kasar Saudiya ta dawowa hukumar NAHCON, don mayarwa maniyatan da basu samu damar zuwa hajjin ba.
A sanarwa ta ce, akwai sama da Naira miliyan daya da dubu biyar wanda za’a baiwa jihohin da basu samu ruwan Zam-Zam ba.
Hukumar ta bukaci wadanda abun ya shafa su je hukumar jin dadin alhazai jihohinsu don karba kudaden na su.

Leave a comment