Shinkafar Da Ake Shigowa Da Ita Nijeriya Tana Da illa Ga Jikin Bil’ ada — Inji lai Muhammed

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mafi yawa daga cikin shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen ketare tana da illa ga jikin bil adama.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed , yayin wani taron manema labarai a garin Oro da ke yankin karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.
Ya ce akwai bayanan da suka samu cewa yawancin shinkafar an noma ne domin amfanin dabbobi amma abin takaici wasu marasa kishin kasa ke safarar su zuwa cikin kasar nan, su sayarwa jama’a.
Alhaji Lai Muhammed ya ce gwamnati ta sanya tsastsauran tsaro akan iyakokin kasar nan domin kula da wadanda ke safarar irin wadannan shinkafa.
A cewar sa, gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana domin ganin cewa kasar nan ta rika iya samar da isasshiyar shinkafa da zai biya bukatun al’ummar ta baki daya

Leave a comment