TATTALIN ARZIKI: Bankin Diamond Ya Shiryawa Masu Kananan sana’o’i Taron Bita

A bisa kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi na kara bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da hanyoyin tallafawa masu kananan sana’o’i a , Bankin Diamond ya hada hannu da babban Bankin Nijeriya CBN da Kamfanin sadarwa na MTN domin samar da hanyoyin tallafawa masu kananan sana’o’i ta yadda zasu inganta kasuwancin su ta hanyar Bude asusun ajiya wanda hakan zai taimaka musu.

A wani taron bita da Bankin Diamond reshen kaduna ya shiryawa kananan da matsakaitar ‘yan kasuwa domin nuna musu hanyar da zasu bi wajen inganta harkar kasuwancin su.

Taron wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Gidan Sardauna da ke jihar Kaduna, Bankin ya bayyana cewa lokaci yayi da kananan da matsakaitar masu sana’o’i zasu bude asusun ajiya ta wayoyin su na hannu wanda hakan zai basu damar siya da sayarwa da sauran hada – hadar kasuwancin Kudi Cikin Sauki ta yin amfani da wayayoyin su na hannu domin bunkasa ci gaban kasuwancin su.

A zantawarta da manema Labarai yayin gudanar da taron , daya daga cikin wakiliyar Bankin Diamond, Halima Gaida , ta bayyana cewa Bankin su ya dauki aniyar taimakawa kananan da matsakaitar ‘yan kasuwa wajen gudanar da harkar shige da fice na kudaden su cikin sauki wanda kuma hakan zai taimaka musu wajen inganta kasuwancin .

Akan hakan Halima Gaiya, ta bukaci matan jihar Kaduna musamman ma masu kananan sana’o’i da su tabbatar da cewa sun bude asusun ajiyarsu da Bankin Diamond, domin kara inganta kasuwancin su ta siya da sayarwa cikin sauki.

Halima , ta kuma zayyana lambobin da masu kananan sana’o’i zasu bude asusun ajiyarsu ta wayar su ta hannu kamar haka: *710# wanda nan take za’a bude musu asusun ajiyar kudi tare da Bankin Diamond.

Ta ci gaba da cewa yanzu haka wakilan bankin suna yawo cikin gari domin nunawa jama’a muhimmancin hada – hadar kasuwancin Kudi ta hanyar Bude asusun ajiya.

Mahalarta taron da dama wadanda aka zanta da su, sun yaba gami da jinjinawa Bankin na Diamond da shirya taron inda suka ce yanzu sun samu ilimi kan yadda zasu bude asusun ajiyarsu, acewarsu, haka zai saukaka musu harkar kasuwancin su.

Leave a comment