Muna Godiya Ga Elrufai Da Sheikh Albani – Kungiyar Majalisar Malaman Allo

An jinjinawa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufai, da Darakta Janar Mai Kula da harkokin Addinai na Jihar Kaduna, Sheikh Jamilu Albani Samaru Zaria, bisa nadin Shugabanin Kwamitin Malaman Tsangaya da Makarantun Allo na Jihar kaduna, karkashin Shugabancin Alaramma Imam Buhari Maraban Jos, da sauran mambonin kwamitin.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wacce ta sami sa hannun jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Malaman Tsangaya da makarantun Allo ta Jihar kaduna, Malam Aliyu Jibril Kura, wanda aka raba ma manema labarai a kaduna.

Sanarwar ta bayyana cewa, a madadin sabon shugaban kwamitin Malaman Tsangaya da makarantun Allo ta Jihar kaduna, Alaramma Imam Buhari Maraban Jos, da sauran ‘yan mambobin kwamitin, muna mika godiyarmu ta musamman ga Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufai, bisa yarda da amincewa da yayi wajen nada shugabanin kwamitin Malaman Tsangaya da Makarantun Allo na Jihar kaduna, da cewa ya zama wajibi a gare mu da mu jinjina ma mai girma gwamnan, a bisa irin wannan Namijin kokari da gwamnan yayi, musamman a dai dai irin wannan lokaci da wasu bata gari ke amfani da sunan malaman allo suna tauye hakki da kuma cin zarafin kananan yara.

Takardar sanarwa ta qara da bayyana cewa, ”tabbas ba zamu gushe ba, sai mun mika godiyarmu da yabo na musamman ga hazikin Malamin Matashi mai kishin jihar kaduna, Sheikh Jamilu Albani Samaru Zaria, a bisa yadda yake jajircewa babu dare ba rana wajen ganin ya dawo da martabar kungiyoyin malamai da addinai a Jihar kaduna. Tabbas wannan abin a yaba masa ne hakkun.”

“Muna mika sakon godiyarmu ta musamman ga Darakta Janar mai kula da harkokin addinai na jihar kaduna, Sheikh Jamilu Albani Zaria, a bisa yadda da amincewarsa a gare mu, domin daura mana wannan babban nauyi na yima addinin Allah aiki. Muna amfani da wannan dama domin nuna godiyarmu a gare shi, da kuma tabbatar masa da cewa, da yardar Allah ba zamu bashi kunya ba, kuma da yardar Allah nan ba da jimawa ba, za a fara ganin sabon tsare tsaren ci gaba da kwamitin zai fara gudanarwa domin ci gaban jihar kaduna baki daya.”

Sabbin Shugabannin kwamitin sun hada da;

Alaramma Imam Buhari Maraban Jos, a matsayin Shugaban kwamitin. Da Imam Haruna Ikara, a matsayin Mataimaki na daya. Da kuma Imam Fathu Umar Fandogari, a matsayin Shugaba na biyu. Sai kuma Goni Nasiru Usman Ja’afar, a matsayin babban sakataren kwamitin. Sai kuma Alaramma Adamu Sa’idu Wakili, a matsayin Mataimakin babban sakatare.

Nan gaba kadan za’a sanar da sauran shugabannin kwamitin kananan hukumomi.

Leave a comment