Sarkin Karaye Ya Rushe Majalisar Masarautarsa

Sarkin karaye Alhaji Ibrahim

Daga Nasiru Salisu, Kano

Sarkin Karaye da ke jihar Kano Alhaji Ibrahim Abubakar ya sanar da cewa ya rushe majalisar masarautar sa saboda wasu dalilai.

Sarkin ya jaddada aniyarsa ta fadada mukaman a cikin kananan hukumomi takwas 8 na Masarautar, tare da alkawarta cewa wasu daga masu rike da mukaman za su dawo yayin da wasu kuma za a daga likkafarsu zuwa gaba.

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya rushe majalisarsa bayan kammala wata ganawa da duk masu rike da mukamai a Masarautar.

Babban dan majalisar Sarkin Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmad ne ya sanar da hakan, sai dai ya ce rushewar ba ta shafi wasu Hakimai guda takwas na Masarautar ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Karaye Haruna Gunduwawa ya fitar a jiya.

Ya kuma jinjinawa ‘yan majalisar ta sa bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da Masarautar ta Karaye gaba.

Leave a comment