Rundunar ‘Yan Sandar Jihar Kano Ta sake Ceto Wani Yaro A Anambra

Daga Nasiru Salisu, Kano

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta ceto wani yaro dan shekara 11 da aka sace daga unguwar PRP da ke unguwar brigade a nan Kano, a shekara ta 2014 aka kuma sayar da shi a jihar Anambra.

Kakakin rundunar ta ‘yan sanda DSP Abdullahi Haruna ya ce Paul Onwe da Mercy Paul ne suka sace tare da sayar da yaron mai suna Muhammad Ya’u, a kan kudi naira dubu dari biyu.

Ya kara da cewa tuni aka mayar da Muhammad Ya’u addinin Krista aka kuma canza masa suna Chinedu Ogbodo daga hannun wadanda suka saye shi.

Rahotannai na nuni da cewar tuni aka kama wadanda ake zargin da sace yaro su uku, inda kuma yanzu haka suke karkashin binciken ‘yan sandabinciken ‘yan sanda , biyo bayan yara tara da aka ceto a yan kwanakin nan.

DSP Haruna ya ce rundunar na iya kokarinta wajen ceto yara yan Kano da aka sace tare da sayar da su a jihar ta Anambra

Leave a comment