ZABEN KOGI: Dan Takarar PDP Yayi Watsi Da Sakamakon Zabe.

Dan Takarar PDP

Daga Mohammed A. Mohammed

Dan takarar gwamna a babbar jam’iyyar hamayya wato, PDP ya yi watsi da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar ranar Asabar a jihar Kogi.

A wata sanarwa da ya fitar, Injiniya Musa Wada ya ce da shi da magoya bayansa masu dimbin yawa a jihar ba su amince da sakamakon zaben 16 ga watan Nuwamba ba.

Ya ce a ganinsa, ba zabe aka gudanar ba illa ‘ayyana yaki kan al’umma’.

Ya kuma zargi jami’an tsaro da hada kai da gwamnati wajen tsoratar da mutane da kashe masu kada kuri’a, inda ya ce mutanen da suka rasa rayukansu ba su gaza 9 ba.

Ya ce tun da aka sanar da Yahaya Bello a matsayin wanda ya yi nasara, al’ummar jihar ke alhini.

Injiniya Musa Wada ya ce zai bi hakkinsa a kotu kuma ya ce shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Mahmoud Yakubu da Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu za su yi bayani a gaban Allah kan rawar da suka taka a zaben da ya ce mai cike da magudi.

Gwamna Yahaya Bello

Leave a comment