Muna Goyon Bayan Rufe Kan Iyakokin Nijeriya-  Manajan Sa’afa Rice

Alhaji Gali Ibrahim
Akokarin da gwamnatin Nijeriya keyi na bunkasa noman shinkafa, wanda hakan ya sanya gwamnatin rufe kan Iyakokinta domin hana shigowa da shinkafa daga kasar waje, kamfanonin sarrafa shinkafa a kasar sun yaba da matakin Gwamnatin.
Kamfanin Sarrafa Shinkafa Na Sa’afa Rice, yana daga cikin kamfanonin da suke samar da shinkafa ‘yar gida, wanda suka bayyana matakin shugaba Buhari na rufe daukacin Iyakokin Nijeriya, inda suka ce hakan zai taimaka wajen kawo bunkasar tattalin arzikin kasar.

Manajan Kamfanin Alhaji Gali Ibrahim ‘Yan Doya, ya bayyana goyon bayansu kan rufe iyakokin kasar nan, inda suka ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Alhaji Gali Ibrahim ‘Yan Doya, ya kuma yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan rufe iyakokin domin hana shigo da abubuwan da ake iya sarrafawa a cikin kasa.
Alhaji Gali, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a kamfanin dake Kan hanyar Bunkure a jihar kano.
Da yake bayani akan shinkafar da suke samarwa, Gali Yace” muna samar da shinkafa mai kyau wacce duk wanda yayi amfani da ita zai tabbatar da hakan.

Shugaban kamfanin Sa’afa Rice Alhaji Auwalu Musa A Bakin Aiki

Ya ci gaba da cewa ” Mun samar da inijina masu kyau da inganci irin na.zamani masu gyara shinkafa wanda ko ta ta kasar waje bata fita ba.
Akan hakan, Manajan ya bukaci daukacin al’ummar kasar nan da su ci gaba da bawa gwamnatin kasar goyon da suka kamata akan rufe Iyakokin wanda yin hakan alheri ga ci gaban kasar baki daya.

Leave a comment