CUTAR KORONA: Sule Lamido Ya Mika Kansa Don Yi Masa Gwaji A Kano

Daga Nasiru Salisu,Kano

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce an yi masa gwajin cutar korona, a jihar Kano.A sakon da ya wallafa a shaifinsa na Facebook ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce daraktan kiwon lafiya na ma’aikatar lafiyar jihar Kano, Dr Imam Wada Bello ne ya aika masa da sakon da ke neman ya mika kansa a yi masa gwaji saboda ya halarci jana’iza ranar Alhamis wacce shi ma mutumin nan da aka gano yana dauke da cutar a Kano ya halarta.”Muna so ka ba mu dama mu gwada ka domin ganin ko akwai yiwuwar kana cikin hatsarin kamuwa da cutar”, in ji sakon.Gwamnan ya ce da misalin karfe daya da rabi na ranar Litinin shi da direbansa da jami’in tsaron da ke ba shi kariya aka yi musu gwajin coronavirus.Ya ce suna jiran sakamakon gwajin.

Leave a comment