Gwamna Bala Mohammed Ya Ba Shugaban  Kungiyar NUJ Da NAWOJ Kyautar Mota

Daga Shehu Yahaya

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya Bawa shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta jihar NUJ da takwararsa Ta NAWOJ Kyautar mota kirar Peugeot 406 da Ford Galazy.
Da yake mika Kyautar, Gwamna Bala Mohammed, yace Tun lokacin da ya cika kwanaki 100 a kan karagar kujerar Gwamnan jihar Bauchi yayi alkawarin bayar da Kyautar motar ga shugabannin biyu wanda yau ya cika alkawarinsa.

Gwamna Bala, wanda shugaban ma’aikata a fadar Gwamnatin jihar, Dakta Ladan Salisu, ya wakilta, ya godewa shugabannin ‘yan jaridu bisa gudunmuwa da suke Bawa gwamnatin jihar na fadakar da al’ ummar jihar akan ayyukan ci gaba da gwamnatin take aiwatar wa.
Taron wanda aka gudanar dashi a fadan gwamnatin jihar, ya samu halarcin manyan jami’an gwamnatin jihar Bauchi da ‘yan jaridu.

A nasa jawabin shugaban kungiyar ta NUJ na jihar Bauchi Umar Sa’idu, ya godewa Gwamnan bisa Kyautar da yayi musu inda yace NUJ da NAWOJ zasa ci gaba da Bawa gwamnatin shawara akan kawo abubuwan ci gaba a fadin jihar.
Akan hakan ya bukaci Gwamnan da ya rinka amsar suka mai ma’ana daga wurare daban- daban wanda hakan zai taimaka wajen kara kawo ci gaba mai dorewar a fadin jihar baki daya.

Leave a comment