Cibiyata ta Inganta Rayuwar Jama’a za ta tallafawa ‘Yan Najeriya – Oluremi Tinubu

Sanata Oluremi Tinubu da Hajiya Nana Shettima

Daga Ibraheem Hamza Muhammad

Cibiyar Inganta Rayuwar Jama’a, wacce a Turance ake Kira da suna ‘Renewed Hope Initiative’ (RHI) ta ‘kuduri aniyar rage kuncin rayuwa ga al’ummar Najeriya.

Ta fa’di hakane bayan taron hukumar gudanarwa ta Cibiyar da aka gudanar a ofishinta fake cikin Fadar Shugaban ‘Kasa ta Aso Rock dake Abuja.

Wannan sanarwa ta biyo bayan sanarwa da kakakinta Busola Kukoyi ta fitar.

Uwargidan Shugaban ‘Kasa Ahmed Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu wacce itace Shugabar Cibiyar don Inganta Rayuwar Jama’a ta ce, an kammala tsari domin ‘kaddamar da shirin a jihohi 36 da babban birnin Tarayya, Abuja.

Barr Chioma Uzodinma, Dr Beta Edu, Hajiya Nana Shettima, Sanata Oluremi Tinubu, Ekaette Unoma Akpabio, Salamatu Gbajabiamila, da Farfesa Hafsat Ganduje.

Ta furta cewa za a sanya Matan Gwamnoni da na Shugabannin ‘Kananan Hukumomi a cikin shirin.

Sanata Oluremi Tinubu ta Kara da cewa, ana son tabbatar da ganin wa’danda za su ci moriyar shirin an yi musu rajista da tantancesu domin su ci moriyar shirin don samun tallafi da fita daga ‘kuncin talauci.

Bugu da’kari, ta ce za a fara raba tallafin ne daga ragowar ku’din da ya yi saura daga ku’din kamfen din 2023 kafin a nemo tallafi daga ‘Yan Kasuwa da hukumomi da cibiyoyi masu bada tallafi na Duniya.

Sanata Oluremi Tinubu ta ce, “Shirin zai ba da damar a tallafawa talakawa, don su ci ribar romon mulkin Dimokradiya muraran.”

Uwargida Oluremi Tinubu za ta yi taro da Matan Gwamnoni ran 14 ga wannan wata na Yuli domin tsara yadda shirin zai kai ga cin nasara gadan-gada.

Taron ya sami halartar Mataimakiyar Shugabar Cibiyar Kuma Uwargidar Mataimakin Shugaban ‘Kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima; da Sakatariya Kuma Uwargidar Gwamnan jihar Imo, Misis Chioma Uzodinma, da Uwargidar Shugabar Majalisar Dattijai, Unoma Akpabio; da Uwargidar Shugaban Ma’aikata a ofishin Shugaban ‘Kasa, Salamotu Gbajabiamila; da Shugabar Mata ta Jamiyyar APC, Dr Betta Edu da Kuma Farfesa Hafsat Ganduje wadanda sune jagororin Cibiyar.

Leave a comment