Muna Samar Da Ingattaccen Takin Zamani Ga Manoma-Dan Sabo

Daga Shehu Yahaya

Kokarinsa na samar da takin zamani mai inganci kuma mai saukin farashi ga dauka in manoman kasar nan, Kamfanin samar da Takin zamani na  DAN SABO dake jihar Kano A Arewacin Nijeriya, ya yi alkawarin samar da Taki wadatacce ga manoma a fadin kasar nan baki baya.

Kamfanin na  DAN SABO, ya bada tabbacin cewa zai samar da taki wanda zai zama mai inganci daidai da yanayin kasar noman da ake da ita, bisa farashi mai sauki da kuma inganci tare da wadatar da takin a duk lokacin bukatarsa ta taso zuwa wasu jihohi dake fadin Nijeriya.

A zantarwasa da manema labarai a Hedikwatar Kamfanin dake jihar Kano, Shugaban amfanin na DAN SABO Alhaji Kabiru Sabo, ya bayyana cewa kamfaninsu ya kudiri aniyar samar da takin zamani mai inganci da Nagarta wanda duk manomin da yayi amfani dashi zai samu amfani mai yawa. 

Shugaban  yace sun shirya tsaf domin samar da wadataccen taki ga manoma wanda zai zama mai inganci daidai da yanayin kasar noman da ake da ita, bisa farashi mai sauki

Alhaji Kabiru Sabo, wanda yana daga Cikin shugabannin  Kungiyar masu masu kananan Kamfanin taki ( SMALL SCALE FERTILIZER  COMPANIES) na jihar Kano, ci gaba da cewa “Wannan kamfanin yayi Tannadice mai kyau domin samar da taki mai inganci ga manoma wanda kuma duk wanda yayi amfani dashi zai Ci moriyar amfanin gonansa” inji shi.

Acewarsa kamfaninsu yana samar da aikin yi ga matasa  masu yawan gaske  wadanda suke aiki kai tsaye da kamfanin zuwa ‘yan sarin kayanssu da kuma ‘yan talla, wanda mafiyawan wadanda zasu amfana manoma ne, da matasa masu neman sana’a.

.

Leave a comment