TSARO: Sarkin Kano Ya Bukaci Hakimai Da Su Marawa Jami’an Tsaro Baya Wajen Dakile Ayyukan Bata Gari

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Daga Shehu Usman Yahaya

Sabon Kwamandan Hukumar Tsaro a cikin Al’uma wato (Civil Defence) a jihar Kano ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano domin neman goyon bayan masarautar ta yadda za’a inganta harkokin tsaro.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Hakimai da dagatai da masu unguwarni su marawa yunkurin Hukumar tsaro ta cikin al’umma baya wato (Civil Defence) domin samun nasarar kakkabe bata gari dake cikin al’umma.

Mai Martaba sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yaKe karbar ayarin shugabanin gudanarwar hukumar tsaro ta cikin al’ umma (Civil Defence) bisa jagorancin sabon kwamandan hukumar Muhammad Lawan falala afadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana yunkurin hukumar tsaro ta cikin al’umma da cewa ya dace, duba da ganin irin yadda take gudanar da aikin ta ba dare ba rana.

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Daganan sai yaja hankalin daukacin al’ummar jihar Kano su himmatu Wajen gudanar da addu’oi na musamman domin samun cigaban dorewar zaman lafiya a jihar kano dama kasa baki.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yiwa sabon kwamandan fatan Alkhairi ayayin gudanar da aikinsa tareda samun nasara.

Tunda farko da yake jawabi, sabon kwamandan hukumar tsaro ta cikin al, umma wato civic Defence, Muhammad Lawan falala, yace sun Kawo wannan ziyarar ne ga Mai martaba sarki domin gaisuwar bangirma tare da neman tabaraki da sanya albarka.

Lawan falala, ya bayyanawa sarkin Kano yunkurin hukumar don haka yake Neman hadinkai da goyon bayan masarautar kano domin samun nasarar cimma burin da akan sanya a gaba na wajen dakile masu aikata miyagun laifuka a cikin al’uma.

A yayin ziyarar dai sabon kwamandan hukumar yana tare da manyan Jami’an gudanarwar hukumar ta jihar kano.

Leave a comment