KARANCIN RUWAN SAMA: Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Yayi Umarnin A Tashi Tsaye Domin Yin Addu’oi

Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano

Daga Shehu Usman Yahaya

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi umarni da a dage da ci gaba da addu’a domin rokon Allah ya kawo dauki kan karancin ruwan sama da ake fuskanta a sassan jihar Kano.

A wata sanarwa da aka fitar, Mai Martaba Sarkin ya umurci dukkanin Limaman Masallatan juma’a da ke jihar Kano su gabatar da addu’o’i na musamman a dukkanin masallatan da su ke jagoranta
don neman yardar Allah ya bamu ruwan sama mai albarka, a jihar Kano da kewaye.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma bukaci dukkanin Masallatan hamsas salawati da malaman makarantun islamiyyu da na tsangayu suma su yi addu’ar samun ruwan saman ba tare da jinkiri ba.

Ya kuma umurci dukkan Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni da dukkan shugabannin al’umma da ke fadin jihar nan, su hada kan al’ummar Musulmi a yankunansu domin kai kuka wajen Allah subhanahu wa ta’ala ya yaye halin ƙunci da ake ciki musamman na rashin ruwa da tsadar abinci da rashin tsaro da ake fuskanta a birni da kauyukan mu.

Ya kuma shawarci dukkanin iyaye da su sanya idanu tare da jan kunnen ‘ya’yansu dasu guji aikata rashin da’a da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yawaita tuba ga Allah bisa laifuka da ke gudana wadanda muka sani dama wadanda ba mu sani ba.

Daga nan Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci dukkanin ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah tare da gudanar da harkokin kasuwancin su ta hanyar da shari’ar Muslunci ta tanada.

Haka kuma ya yi kira ga Gwamnati da bin dukkan hanyoyi da suka dace don saukakawa al’umma da Ubangiji Ya ba mu jagorancin su.

Leave a comment