Muna tuna yaranmu ne da suka rasa rayukansu — Inji Maryam Gashuwa

Daga Fatima Idris, Kaduna

Kamar yadda suka saba a duk shekara, Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda aka fi sani da ‘yan shi’a suna gudanar da taron tunawa da taron da suka kira da ‘waƙi’ar Ƙudus’ wacce ta auku a ranar 25 ga watan Yulin 2014 a garin Zariya.

A bana ma ba su yi ƙasa a guiwa ba, inda suka gabatar da taron bayan shekaru tara da aukuwar lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar 2014 ne a yayin zanga-zangar lumana domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a garin Zariya, sojoji suka afka ma mabiya Harkar Musuluncin inda suka kashe mutum 34 ciki harda ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky guda uku da wani kirista mai suna Julius Anyanwu da wani mutumin gari da ya taso daga wurin aiki.

A yayin ganawa da manema labarai a yayin taron, dan uwan Shaikh Zakzaky, Badamasi Yaqoub ya bayyana makasudin taron da cewa;
“Tunawa da shahidanmu wanda aka kashe su shekara kamar tara (9) da suka wuce. Wato wannan waki’ar ya faru ne a nan Zariya wanda ya zama an kashe mutum 34. Akwai kirista guda daya. Akwai ‘ya’yanmu guda uku shi ne; Ahmad, da Hamid da Mahmud”.

Ya ƙara da cewa; “muna nan ne domin tunawa da gwaraza wadanda ainihin aka kashe su saboda bin tafarkin Allah”.

Ya ci gaba da cewa; “haka hanyar addini take, ba ta canjawa. Zan iya tunawa na je wajen wani Ayatullah a Iraƙi sai yake ce min Saddam ba wani gidan da bai kashe mutum ba, amma yau Saddam ya zama tarihi. Haka ma duk wani Fir’auna da zai tsaya ya yi Fir’aunanci ya kan zama tarihi ne kawai. A don haka kowanne azzalumi akwai ranar karshen shi.

Kazalika, Sister Maryam Gashuwa, shugabar Gidauniyyar tallafawa marayun da aka kashewa iyaye da ‘yan’uwa da ‘ya’ya, ta ce sun tarune don tunawa da yayansu da aka kashe wandata tabbatar da hakan na cikin cikin aikace-aikacensu.

Gashiwa ta kara da cewa aikinsu ya haɗa da lura da nauye-nauye da yawa. Kamar ita Mu’assatus Shuhada tana daukar nauyin iyalan shahidai, misali karatun ‘ya’yan shahidai, wani lokaci rashin lafiyarsu, sannan abinci, wani lokaci akan tallafa, amma ba ana yi ɗari bisa ɗari ba”, in ji ta.

Sister Maryam ta ce daga cikin waɗanda suke amfana da wannan tallafin ya haɗa da iyaye, ‘ya’ya da matan da aka kashe mazajensu, da akalla sun kai dubu biyu.

Taron na bana ya gudana ne a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ta jihar Kaduna. Wanda aka soma da misalin ƙarfe 8 na safe da saukar Alƙur’ani mai girma wanda Madrasat Darur Imam Mahdi ta gabatar. Sannan aka buɗe taron da addu’a wanda Malam Musa Tudun Jukun ya yi, sannan Mahdi Salihu Garba ya karanto ayoyi daga Alkur’ani mai girma.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya

Leave a comment