Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Fita Neman Magani A Kasar Waje

Daga Muhammad Abdullahi

Jagoran Mabiya Harkar Musulunci A Nijeriya, Sheikh Ibrahim Yaqub Al-Zakzaky Tare Da Uwargidansa Malama Zeenatudden Ibraheem, Sun Kama Hanyar Tafiya Ƙasar Waje Domin Neman magani.

Da misalin karfe bakwai na yammacin yau Talata ne agogon Nijeriya, Shehin Malamin tare da me dakin shi suka tashi a jigin sama kanfanin Qatar Air, ta babban filin sauka da tashin jiragen sama na babban birnin Tarayya da ke Abuja, domin fita neman lafiya.

Idan ba ku manta ba, a shekarar 2015, lokacin mulkin Shugaba Buhari, Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky, ya sami munanan raunuka tare da iyalinshi daga harbin bindiga, inda aka kashe sama da mutane dubu daya ciki harda ‘ya’yansu guda uku a garin Zaria, bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da taimakon tsohon gwaman jihar Kaduna, Nasiru Elrufai

Leave a comment